EFFC tace bata Sami Rigar Mama ta Gwal Cikin kadarorin Diezani ba

Date:

Shugaban hukumar yaƙi da rashawa a Najeriya (EFCC) ya musanta rahotannin da ke yawo cewa akwai rigar mama ta gwal a cikin kayan da hukumar ta ƙwace daga hannun Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar man fetur ta Najeriya.

Ana zargin Diezani wadda ta fice daga Najeriya a 2015 da satar kuɗin da suka kai dala biliyan biyu da rabi daga asusun gwamnatin ƙasa a lokacin da take minista, kodayake ta musanta zargin.

A watan Mayu ne Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya faɗa wa Majalisar Wakilai cewa darajar sarkoki da awarwaro da sauran kayan ƙawa da aka ƙwace daga wurin Diezani ta kai naira biliyan 14.

A watan Oktoba gwamnatin tarayya ta lissafa wasu kadarorinta da ta ƙwace waɗanda suka haɗa da gidaje a Banana Island da ke Ikoyi ta Jihar Legas.

Sai dai da ya bayyana a kafar talabijin ta TVC ranar Laraba, Abdulrasheed Bawa ya ce labarin rigar mama ta gwal da aka ce akwai ta a cikin kayan na ƙanzon kurege ne.

Babu wani abu mai kama da rigar mama ta gwal, maganar ‘yan kafafen sada zumunta ce,” in ji shi.

“Zan iya faɗa muku a kyauta saboda ni ne jagoran wannan binciken. Ban san da ita ba. Idan da akwai ta ya kamata a ce na sani. Ya kamata na sani saboda ni na jagoranci binciken da sauransu.”

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Gaya Polytechnic

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya...

Sojoji sun mikawa Tinubu Shawarwari yadda za a kawo karshen matsalar tsaron Nigeria

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karɓi rahoton dakarun sojan...

Shugaba Tinubu ya sake nada Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da nadin...

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Koma Jam’iyyar APC a Hukumance

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar...