Iftila’i: Ana fargabar cutar kwalara ta hallaka mutane 5 da jikkata wasu a Kano

Date:

Aminu Yahaya Tudun Wada

 

Ana fargabar barkewar cutar amai da gudawa a Unguwar Gama yan alewa dake karamar hukumar Nasarawa a jihar kano wanda har ta yi sanadiya rasuwar akalla mutane hudu zuwa biyar.

A zantawar wakilin Kadaura24 da wasu daga cikin iyayen yara da yan uwan wadanda abun ya shafa sun ce kawai sun wayi gari da garin ya’yansu suna amai da gudawa wanda hakan tasa suka rika garzayawa da su asibiti domin su sami kulawar likitoci.

Ana dai zargin rashin ruwan da ake fama da shi a yankin ne ya haddasa cutar ta amai da gudawa da yanzu haka ke cigaba da addabar al’ummar yankin.

Sai dai sun Iyayen yaran sun koka da yadda likitoci ke kin Karbar marasa lafiyar domin ba su kulawar da ta dace.

Yanzu-yanzu: Kotu a Kano ta baiwa KANSIEC damar gudanar da zaben kananan hukumomi

” Na kawo dana asibitin bitinariya dake unguwar mu, amma likitoci sun ki Karbar su sun ce wai sai dai mu Kai su asibitin zana”. Inji mahaifiyar wani yaro da ta kamu da cutar.

Ta ce Sanadiyar rashin karbar masu amai da gudawar yanzu haka kusan kowane gida akwai majiyanta yara da manya.

Al’ummar mazabar Gama Brigade layin yan alewa bayan bitunariya sun koka da yadda likitocin asibitin sha-ka-tafi na Asibin gama wato Bitunariya suke kymarsu da kuma kira ga Gwamnatin jihar kano data kawo agajin gaggawa domin Akalla kusan mutane dari sun kamu da cutar amai da gudawa.

Talla

Sai dai lokacin da jaridar kadaura24 ta tuntubi mai magana da yawun ma’aikatar lafiya ta jihar kano Ibrahim Abdullahi ya ce ma’aikatar lafiya bata da labarin bullar cutar a yankin, amma za ta bincika domin daukar matakan da suka dace don shawo kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...