Yanzu-yanzu: Kotu a Kano ta baiwa KANSIEC damar gudanar da zaben kananan hukumomi

Date:

Daga Sharifiya Abubakar

 

Wata Babbar kotun jihar kano ta baiwa hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar damar gudanar da zaben kananan hukumomi wanda aka shirya gudanarwa ranar asabar 26 ga watan October.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar talata wata Babbar kotun tarayya dake kano ta rushe shugabanni hukumar Zaɓen tare da bukatar samar da sabbi wadanda suka chanchanta domin gudanar da zaben.

Talla

Sai dai a umarnin da Babbar kotun jihar kano karkashin jagorancin mai Shari’a Sanusi Ma’aji a yau juma’a a baiwa hukumar umarnin cigaba da shirye-shiryen zaben domin ganin an gudanar da zaben a gobe asabar.

Hukumar zaɓe mai zaban kanta ta jihar kano ce dai ta shigar da karar inda take karar jam’iyyar APC da wasu guda 13.

Kamar yadda mai Shari’a Ma’aji ya bayyana hukumar zaben ta jihar kano tana da ikon shiryawa da kuma gudanar da zaben kananan hukumomi 44 kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya bata dama.

Talla

Ya ce yayi watsi da duk wani yunkuri na kawo wa zaben cikas.

Kotun ta kuma umarci dukkanin jami’an tsaro dake jihar da su tabbatar sun samar da tsaro yayin zaben kananan hukumomin na jihar kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...