Cire T-Gwarzo daga Minista: Bashir Gentile ya aikawa Tinubu Sako

Date:

Daga Sharifiya Abubakar

 

Guda cikin na hannun daman tsohon Karamin Ministan gidaje da raya burane Abdullahi Tijjani Gwarzo wato Bashir Hayatu Gentile ya ce Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi Babban kuskure da cire T-Gwarzo daga mukamin Minista.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito shugaban ƙasar Bola Ahmad Tinubu ya sauke wasu daga cikin ministocinsa ciki har da Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo daga jihar Kano.

Talla

A wani sakon murya da Bashir Gentile ya aikowa kadaura24, ya ce babba asara ce cire T Gwarzo daga mukamin Minista kasancewarsa dan Siyasa da al’umma suke amfana da shi matuka.

Da dumi-dumi: Shugaba Tinubu ya sallami ministoci tare da maye gurbinsu da wasu

“Babu shakka jam’iyyar APC ta yi babbar asara, kuma duk wanda ya baiwa Tinubu shawarar cire T Gwarzo daga mukaminsa to ba masoyin Tinubun ba ne , kasancewar T Gwarzo dan Siyasa tun daga tushe da ya jima yana taimakawa al’ummarsa”. Inji Bashir Gentile

Talla

Ya ce duk cikin yan siyasar Kano dake da mukami a Abuja babu wanda al’ummar jihar Kano suke son gani kamar T-Gwarzo saboda shi ne yake Kula da su ya kuma mutunta su ba tare da la’akari da girman mukaminsa ba.

Talla

“T-Gwarzo ya san darajar mutane kuma yana taimakawa al’ummarsa, Sannan yasan nasa, kuma yana shiga sabgogin mutane, yana taimakawa yan jam’iyyar adawa ta Kwankwasiyya ba ballantana yan jam’iyyar ta APC da ma al’ummar jihar Kano baki daya, babu shakka Tinubu ka tabka kuskure”.

Bashir Gentile ya yi fatan shugaba Tinubu zai sake duba matakin da ya dauka akan T-Gwarzo, sannan ya yiwa T Gwarzon fatan alkhairi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...

Zargin kwace gona: Majalisar Dokokin Kano zata binciki Shugabar Karamar Hukumar Tudun Wada (ALGON)

    Majalisar dokokin jihar Kano, ta sha alwashin gudanar da...