Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sallami ministoci biyar tare da naɗa wasu sababbi bakwai da kuma sauya wa goma ma’aikatu.
Wata sanarwa da fadar gwamnatin kasar ta fitar a shafinta na X, ta nuna cewa ministocin da aka cire su ne;

Waɗanda aka sallama:
1-Barr. Uju-Ken Ohanenye; ma’aikatar harkokin mata
2- Lola Ade-John; ministan harkokin yawon buɗe idanu
3- Farfesa Tahir Mamman; ministan ilimi

4- Abdullahi Muhammad Gwarzo; ƙaramin ministan gidaje da raya birane
5- Dr. Jamila Bio Ibrahim; ministar matasa
Waɗanda aka sauya wa ma’aikatu:
1-Hon Dr. Yusuf Tanko Sununu; ƙaramin ministan ilimi ya koma ƙaramin ministan jinƙai da rage talauci
2- Dr. Morufu Olatunji Alausa; ƙaramin ministan lafiya, ya koma ministan ilimi
3- Barr. Bello Muhammad Goronyo, ƙaramin ministan ruwa da tsafta, ya zama ministan ayyuka
4-Hon. Abubakar Eshiokpekha Momoh

Sabbin Ministocin da aka nada :
1- Dr. Nentawe Yilwetde – Ma’aikatar Jin kai
2- Muhammadu maigari dingyadi – Ma’aikatar Kwadago
3- Bianca Odinaka – Karamin Ma’aikatar harkokin kasashen waje
4- Dr. Jumoke Odowale – Ma’aikatar harkokin kasuwancin da zuba jari
5 – Idi Mukhtar Maiha – Ma’aikatar bunkasa harkokin kiwo
6- RT. Yusuf Abdullahi ATA – Karamin Ministan Ma’aikatar gidaje da raya burane
7- Suwaiba Sa’ad Ahmad PhD – Karamar ministar Ilimi