Daga Sharifiya Abubakar
Shugaban kasa Bola Tinubu da majalisar zartarwa ta Nigeriya sun sanar da soke ma’aikatar Neja Delta da ma’aikatar wasanni ta kasa
A wani sako da mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, ya ce an cimma matsayar ne yayin taron majalisar zartarwa ta kasa da aka gudanar a Abuja ranar Talata.

Sanarwar ta ce, “Shugaba Tinubu da majalisar zartarwa ta tarayya sun soke ma’aikatar Neja-Delta da ma’aikatar wasanni ta kasa.
Cikakken bayani kan hukuncin da Kotu ta yi game da zaɓen kananan hukumomin Kano
“Yanzu za a samu ma’aikatar raya shiyoyin Nigeria wadda za ta rika yin aiyukan hukumomin shiyoyin, kamar hukumar raya yankin Neja Delta, hukumar raya arewa maso yamma, hukumar raya kudu maso yamma, hukumar raya arewa maso gabas.”
Ya kuma ce ayyukan ma’aikatar bunkasa wasanni za a mika su ga hukumar wasanni ta kasa, wadda za ta kula da harkokin wasanni a Najeriya baki daya.

“Hukumar wasanni ta kasa za ta karbi aikin ma’aikatar wasanni ta kasa,” in ji shi.
Bugu da kari, majalisar zartarwar ta amince da hade ma’aikatar yawon bude ido da ma’aikatar al’adu da tattalin arziki, tare da samar da hukuma guda da zata rika gudanar da aiyukansu.