Daga Rukayya Abdullahi Maida
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na inganta jin daɗin ma’aikatan gwamnati yayin da ya karɓi rahoton da aka jima ana jira daga kwamitin mafi karancin albashi na jihar.
Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24 a ranar Talata.

Kwamitin, ƙarƙashin jagorancin Usman Bala, mai baiwa Gwamna shawara kan al’amuran jiha, an ɗora masa nauyin duba da kuma bada shawarar inganta tsarin albashi mafi ƙankanta na jihar.
Yayin miƙa rahoton, Gwamna Yusuf ya nuna gamsuwarsa sosai da aikin kwamitin, inda ya yaba musu bisa cikakken bincike da tuntuɓar da suka gudanar.
Gaskiyar abun da ya faru ga yan jaridar gidan gwamnatin Kano har aka sallami wasun su
Ya jaddada cewa shawarwarin kwamitin za su taimaka wa gwamnati wajen aiwatar da manufofi da suka dace da tsarin tattalin arzikin jihar kuma masu ɗorewa.
“Mun zaɓi wannan kwamiti ne saboda muna da imani da ƙarfin basirarsu wajen ba da shawarwari masu fa’ida da sabbin dabaru don ci gaba,” inji gwamnan.

Gwamna Yusuf ya sake tabbatar wa ma’aikatan gwamnati cewa gwamnatinsa za ta cika dukkan alkawurran da ta ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe, musamman wajen inganta jin daɗinsu.
Ya nemi su yi haƙuri yayin da gwamnati ke duba shawarwarin kwamitin a hankali don tabbatar da cewa sun dace da dokokin tsarin mulki.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa za a sanar da hukuncin karshe kan rahoton a mako mai zuwa, inda ya nemi fahimtar dukkan masu ruwa da tsaki yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan lamarin.