Gwamna Abba ya taya Kwankwaso cika shekaru 68 a duniya

Date:

Daga Sani Idris Maiwaya

 

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf taya mai gidansa sanata Rabi’u Musa Kwankwaso murnar cika shekaru 68 a duniya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24.

Talla

Cikin Wani Sako da Gwamnan ya Wallafa a Shafinsa na Sada zumunta Wanda ya dauki hankali Al’umma musamman Yan Siyasa dake Tabbatar da biyayya Ga Mai Gidansa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

“Ya zama wajibi na mika sakon Taya murna kasancewar ka amatsayin jagora kuma shugaba wanda na yi aiki da kai tsawon shekaru 38 da suka wuce”. Inji Gwamnan

Gwamnan ya kara da cewa “lokacin da na yi aiki da Kwankwaso na koyi abubawa dadama wadanda suka taimake ni a Rayuwa dan haka na ke mika sakon taya Murnar zagayowar Ranar haihuwa Mai gidana Shekaru 68 a Duniya”.

Talla

Kwankwaso Wani jigo ne a Siyasa a Kasar nan Wanda Yake da Wasu Muhimman abubuwan koyi na Cigaba ga Al’ummar Kasar nan a cewar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Talla

Ya ce a madadin shi Kansa da iyalansa, gwamnati da al’ummar jihar Kano yana taya tsohon gwamnan murnar cika shekaru 68 a duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...