A watanni 17 da hawan su mulki, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da Mataimakin sa, Kashim Shettima sun yi tafiya sau 41, inda su ka je ƙasashe 26.
![](https://kadaura24.com/wp-content/uploads/2024/10/IMG-20240925-WA0001-300x225.jpg)
A wani bincike da jaridar PUNCH ta yi, Tinubu ya yi tafiya sau 29 zuwa ƙasashe 16, inda ya shafe kwanaki 124 a ƙasashen waje ya kuma shafe awanni 127 a jirgin sama.
Ƙasashen da Tinubu ya ziyarta a halin yanzu sun haɗa da Faransa, Malabo, Equatorial Guinea; London, the United Kingdom (four times); Bissau, Guinea-Bissau (twice); Nairobi, Kenya; Porto Norvo, Benin Republic; The Hague, Netherlands; Pretoria, South Africa; Accra, Ghana; New Delhi, India; Abu Dhabi and Dubai in the United Arab Emirates; New York, the United States of America; Riyadh, Saudi Arabia (twice); Berlin, Germany; Addis Ababa, Ethiopia; Dakar, Senegal, Doha da Qatar.
![](https://kadaura24.com/wp-content/uploads/2024/09/IMG-20240926-WA0041-212x300.jpg)
Shi kuma Shettima ya ziyarci ƙasashe 10 a tifya 12, inda shi kuma ya shafe kwanaki 56 a ƙasashe waje ya kuma shafe awannin 93 a jirgin sama.
A halin yanzu dai Shettima ya ziyarci ƙasashe ƙasashe da suka haɗa da Rome, Italy; St. Petersburg, Russia; Johannesburg, South Africa; Havana, Cuba; Beijing, China; Iowa and New York in the United States of America; Davos, Switzerland; Yamoussoukro, Ivory Coast (twice); Nairobi, Kenya da Stockholm da kuma Sweden.