Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Gwamnatin jihar Kano ta bayar da gudunmawar Naira Miliyan Dari don tallafawa wadanda Iftila’in gobarar tankar mai ta shafa a garin Majiya da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa.
Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da bayar da tallafin a yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai wa Gwamna Umar Namadi Danmodi a gidan gwamnati da ke Dutse ranar Alhamis.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24, gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa an bayar da tallafin ne domin a kai dauki ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma tallafa wa wadanda suka jikkata yayin gobarar.
Gwamnan ya kuma jajantawa iyalan wadanda suka rasu da kuma wadanda suka samu raunuka, inda ya yi addu’ar Allah ya kiyaye afkuwar irin wannan hali a nan gaba.
A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya bayyana matukar godiya a madadin al’ummar jihar Jigawa, inda ya godewa jihar Kano bisa irin gudunmawar da ta bayar a wannan mawuyacin lokaci.
Ya ba da tabbacin cewa za a yi amfani da kudaden cikin adalci wajen taimakon wadanda Iftila’in ya shafa da iyalansu.
Gwamna Namadi ya kuma bayyana cewa, ya zuwa yammacin ranar Alhamis mutane 167 ne suka rasa rayukansu, kuma mutane 67 ke karbar magani a asibitoci daban-daban a ciki da wajen jihar.