APC ta tsayar da Aliyu Harazimi Rano takarar shugaban karamar hukumar Rano

Date:

Hon. Aliyu Harazimi Rano ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC, wanda hakan ya bashi daga zama dan takarar shugaban karamar hukumar Rano a zaɓen da za a gudanar a ranar 26 ga watan nan.

An dai gudanar da zaben ne a jiya asabar da daddare inda bayan gaza samun masalaha a tsakanin yan takarar aka shiga zaɓen tsakanin yan takara 10.

Talla

Bayan kammala kada kuri’u ne Hon. Aliyu Harazimi Rano ya sami nasarar lashe zaɓen da kuri’u tara cikin goma sha shida da aka kada.

Maulidi: Nutsuwa wajibi ga duk masu Musulmi a yayin ambaton Manzon Allah- Malam Ibrahim Khalil

Jim kadan bayan lashe zaɓen, jaridar kadaura24 ta zanta da Aliyu Harazimi Rano wanda ya godewa Allah dangane da wannan nasarar da ya samu, Sannan ya godewa shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a karamar hukumar bisa goyon bayan da suka bashi.

“Ina Mika godiya ta musamman ga jagoranmu Dr. Yusuf Jibril JY tsohon kwamishinan gona na jihar kano bisa gudunnawar da yake baiwa jam’iyyar APC don ta sami nasara”.

” Ina kira da dukkanin waɗanda muka yi takarar da su da su zo mu hada hannu wajen guda domin ceto al’ummar karamar hukumar bisa halin da jam’iyyar NNPP ta sanya su a ciki”. Inji Harazimi Rano

Yace idan yan takarar suka taimaka masa zai iya sami nasarar lashe zaɓen shugaban karamar hukumar ta Rano, don haka yace yana bukatar gudunnawar kowanne daga Cikinsu domin su hada kai don ciyar da karamar hukumar gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano za ta fara jiyo ra’ayoyin al’umma kafin gudanar da duk wani aiki a jihar – Bilkisu Indabo

Daga Samira Hassan   Gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin nan...

Kwankwaso ya gana da Tinubu a fadar shugaban kasa

Daga Nasiba Rabi'u Yusuf   Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso,...

Neman Ilimin addini dana boko da sana’a ba kishiyoyin juna ba ne – Dr. Aminu Sagagi ga matasan Zango

Daga Rahama Umar Kwaru   Wani Malamin addinin musulunci a kano...