Daga Kamal Yahaya Zakaria
A wani mataki na gyara dangantakarsa da jagororin jam’iyyar NNPP, a Kano, Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya gana da ‘yan majalisun tarayya na jam’iyyarsu a Abuja.
Daga Cikin wadanda suka gwamnan ya gana da su akwai wadanda ake ganin sun dade da fusata da yadda Ake mu’amalantarsu a jam’iyyar.
Gwamnan ya wallafa a shafin sa na Facebook, cewa an gudanar da taron ne domin tattauna muhimman batutuwan da suka shafi jihar Kano da jam’iyyar.
DAILY POST ta tattaro cewa sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, AbduRahman Kawu Sumaila, da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Kano kuma dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Rano Kibiya da Bunkure, Kabiru Alhassan Rirum, da sauran su na gab da barin jam’iyyar NNPP.
Yanzu-yanzu : NNPC ya kara kudin litar mai a Nijeriya
Dalilinsu na son barin jam’iyyar NNPP, kamar yadda rahotanni suka bayyana, shi ne yadda ake zargin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso, da gwamnatin Abba Kabir Yusuf sun kaskantar musu da masarautar Rano inda aka mayar da Sarkin mai daraja ta biyu maimakon mai daraja ta daya.
Hakazalika, wasu yan jam’iyyar NNPP na zargin Sanata AbduRahman Kawu Sumaila, da gaza basu gudunmawar da ta dace yayin Shari’ar da aka gudanar bayan rantsar da gwamnatin jihar Kano da kin shiga al’amuran jam’iyyar da gwamnati a lokuta daban-daban.
An baiwa Ganduje wa’adin Kwanaki 7 ya sauka daga mukamin shugaban APC na ƙasa
Sai dai a lokuta daban-daban an jiyo Sanata Kawu na kare kansa a shafukan sada zumunta, inda ya tunatar da masu zarginsa yadda ya lallasa Sanata Kabiru Gaya har ya lashe kujerar Sanatan Kano ta Kudu da Kuma nasarar da ya Samu a kotuna daban-daban.
A nasa bangaren, dan majalisar wakilai mai wakilar Rano Kibiya da Bunkure, Kabiru Alhassan Rirum, ya kalubalanci gwamnatin jihar bisa dawo da sarkin Rano mai daraja ta biyu. Inda ya dage cewa har yanzu yana ganin Sarkin Rano a matsayin Sarki mai daraja ta daya.
Sai dai Gwamna Abba Kabir Yusuf bai taba cewa komai akan batun ba har jiya talata da ya gana da da duk wasu jiga-jigan jam’iyyar NNPP da ke cikin gidan Gwamnan Kano da ke Abuja.