Daga Sani Idris Maiwaya
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar NNPP ta kasa, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya taya gwamna Abba Kabir Yusuf murnar samun lambar yabo ta NUT Golden Award da kungiyar malamai ta Najeriya NUT ta karrama da ita, bisa gagarumar gudunmawar da ya bayar a fannin ilimi.
A wani sako da ya wallafa a sashin shafin sa na X (Twitter) , Kwankwaso ya yabawa Gwamna Yusuf bisa jajircewarsa na farfado da harkar ilimi a Kano.

Ya bayyana gwamnan a matsayin mai Kwarzo a fannin ilimi tare da kara masa kwarin gwiwa da ya jajirce wajen ganin ya ci gaba da kawo sauye-sauye a fannin ilimi a Kano.
“Ina taya mai girma Abba Kabir Yusuf murnar karramawar NUT Golden Award bisa nasarorin da ya samu a fannin ilimi,” in ji Kwankwaso.
Da dumi-dumi: Jarumi Adam A Zango ya sami Mukami
Ya kuma bukaci gwamna Yusuf da ya karfafa kudurinsa na cimma manyan manufofinsa na sake fasalin ilimi a jihar.
Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito an bayar da kyautar ne a yayin bikin ranar malamai ta duniya na 2024, wanda ya gudana a dandalin Eagle Square dake Abuja.

Kungiyar ta NUT tare da hadin gwiwar ma’aikatar ilimi ta tarayya ne suka shirya taron, taron ya hada malamai da shuwagabannin ilimi daga sassan Najeriya domin karramawa tare da nuna matukar farin ciki da nasarorin da aka samu wajen kawo sauyi a fannin ilimi.