Tsohon hadimin Buhari a Kano ya kalubalanci kalaman Kwankwaso akan Peter Obi

Date:

Daga Kamal Yahaya Zakaria

 

Tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari kan harkokin kafafen sada zumunta Bashir Ahmad ya ce Peter Obi ya fi Rabiu Musa Kwankwaso nauyi a siyasance.

Kadaura24 ta rawaito Bashir Ahmad ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafin sa na X.

Talla

Ya rubuta cewa: “Duk da cewa ban taba zama dan Kwankwasiyya ba, amma a koyaushe ina sha’awar Sanata Rabi’u Kwankwaso tare da girmama shi kuma ina ganin sa a matsayin daya daga cikin jiga-jigan siyasar da muke da su a kasar nan.

Ranar Malamai: Wanne Hali Malamai Su ke Ciki a Nigeria

Sai dai ban yarda da kalaman da ya yi kwanan nan a kafafen yada labaran Kano ba, inda ya ce ya fi Peter Obi girma a siyasance.

Ya ce “Kalli sakamakon zaben shugaban kasa na 2023, Peter Obi ya samu kuri’u 6,101,533 kuma ya ci jahohi 11, wanda ya nuna yana da goyon bayansu. Sabanin yadda Sanata Kwankwaso ya samu kuri’u 1,496,687 kuma jihar kano kadai ya ci.

Talla

“Wadannan alkaluma sun nuna a fili cewa, a kalla a yanayin zaben 2023, Peter Obi yana da matukar tasiri a siyasance a fadin kasar nan.

Don haka Peter Obi ya fi Rabiu Kwankwaso girma a siyasance.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...