Ranar Malamai: Wanne Hali Malamai Su ke Ciki a Nigeria

Date:

Yayin da ake bikin Ranar Malaman Makaranta ta Duniya ta bana- 2024, Malamai a Najeriya na bayyana ƙorafe-ƙorafe game da mawuyacin yanayi da suke koyarwa a kasar.

Mafi yawancinsu dai na bayyana damuwa ne a kan abubuwa kamar su rashin biyan kuɗaɗen alawus da rashin yanayi mai kyau a makarantu da kuma ƙarancin albashi, waɗanda suka ce hakan na matuƙar shafar aikinsu.

Talla

Ranar Malamai ta Duniya a bana na mayar da hankali ne a kan buƙatar magance matsalolin da ke ci wa malamai tuwo a ƙwarya da samar da ƙarin damar tattaunawa kan aikinsu na bayar da ilimi, wadda ta haka ne ake ganin za a iya cimma burin da aka sanya a gaba.

Wani malami a jihar Kano ya bayyana wa BBC cewa yana alfahari da kasacewarsa a matsayin malami, amma ya buƙaci hukumomi a matakai daban-daban da su sake lale kan yadda ake tafiyar da harkokin ilimi a ƙasar.

Mutane 7 sun rasu sakamakon Cutar kwalara a Kano

Ya ce: ”Haƙƙi ne a kanmu mu tarbiyantar da yara, mu ilmantar da su , amma babban burinmu shi ne mu ga cewa an ƙara taimaka wa malamai wurin ƙara masu ƙwarin gwiwa musamman ta hanyar yi masu ƙarin girma don ta haka ne za a tabbatar da cewa malami zai yi iyakacin ƙoƙarinsa wurin yin duk abin da ya dace a ɓangaren koyo da koyarwa.”

Akasarin malamai da ke koyarwa a makarantun Najeriya sun koka kan yadda suke ganin hukumomi ba su darraja su yadda ya kamata, lamarin da ke jaddada kiran da suke yi na a gaggauta fitar da tsare-tsaren da za su tabbatar da cewa ana sauraron abin da malamai ke cewa wajen shawo kan ƙalubalensu, kamar yadda wani malami ke ƙorofin cewa ya shafe shekaru da dama yana aikin koyarwa amma a sau ɗaya kacal ya taɓa samun horo na musamman kan aikinsa.

”Na kai shekara 22 ina koyarwa, amma sau ɗaya aka taɓa yi mun ‘training’ a shekarun farko da na fara wannan aikin, wanda na je na amfana na kuma dawo na amfanar da yaran da nake koyarwa, tun daga wannan lokacin kuma ba a sake samun irin wannan damar ba.” In ji shi

Talla

Ranar Malamai dai na tunawa ne da bikin amincewa da kundin shawarwarin hukumar kula da Ilimi da kimiyya da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) da ƙungiyar ƙwadago ta Duniya na shekarar 1966 dangane da matsayin malamai, wanda ya ajiye mizani game da haƙƙoƙi da nauyin da ke rataye a wuyan malamai da kuma ajiye wani tsari na matakin farko da na ƙaro ilimi da ɗaukar aiki da yanayin koyo da koyarwa.

A bana dai ana wannan biki ne a daidai lokacin da matsalolin malamai a ƙasashe masu tasowa, ciki har da irin su Najeriya, ke ƙaruwa, ga kuma matsin tattalin arziki, duk kuwa da irin ƙoƙari da hukumomi ke cewa suna yi na kyautata ɓangaren ilimin, amma koken da malaman ke yi na ƙara fito da zahirin matsalolin, da ya kamata mahukunta su gaggauta magance su don samun nagartacciyar al’umma.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...