Gwamnan Kano ya kaddamar da rigakafin cutar Polio ta shekarar 2024

Date:

Daga Kamal Yahaya Zakaria

 

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da shirin kawar da cutar shan inna na shekarar 2024 a hukumance a karamar hukumar Dawakin Kudu, inda ya jaddada aniyar gwamnatinsa na yaki da cutar shan inna da sauran cututtukan dake addabar yara.

Gangamin wani mataki ne na ganin an yi wa duk yaran da suka cancanta allurar rigakafin kamuwa da cutar domin dakile yaduwar cutar, musamman ganin cewa Kano ta kasance daya daga cikin jihohi 18 da ake samun masu Cutar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa kadaura24 a ranar Asabar.

Talla

A jawabinsa gwamna Yusuf ya bayyana aniyar gwamnatin jihar na kara zage damtse wajen gudanar da allurar rigakafin, tare da hada kai da hukumomin lafiya da al’ummar jihar kano domin rigakafin ta isa ga kowane lungu na Kano.

“Mun kuduri aniyar ci gaba da sanya ido tare da tabbatar da cewa ana ci gaba da yin alluran rigakafi ta yau da kullun don kare yaranmu,” in ji shi

Na Fara Cimma Burina na Farfado da Martabar Gidan Rediyon Jihar Kano – Abubakar Adamu Rano

Ya kuma yi kira ga iyaye da su yi amfani da wannan damar wajen yi wa ‘ya’yansu allurar rigakafi da kuma kula da tsaftar yaran da ta muhallansu domin kare lafiyar al’umma.

Gwamna Yusuf ya godewa duk masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suke bayarwa don samun nasarar Shirin.

Talla

 

Ya kuma ba su tabbacin gwamnatinsa zata cigaba da ba da goyon baya ga duk shirye-shiryen kiwon lafiya da nufin inganta rayuwar al’ummar Kano.

Mataimakin Gwamna Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin yaki da cutar shan inna na Jiha, ya yaba da jajircewar gwamnan kan harkokin kiwon lafiya.

Talla

A nasa jawabin kwamishinan lafiya Dr. Abubakar Labaran Yusuf ya bayyana cewa an zabi Dawakin Kudu a matsayin wurin da za a kaddamar da rigakafin saboda kalubalen kiwon lafiya dake damun yankin.

Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II wanda Dokta Bashir Muhammad Dankadai ya wakilta, ya jaddada bukatar wayar da kan jama’a sosai, inda ya bukaci magidanta da su rungumi allurar riga-kafi ta yau da kullum a matsayin hanyar kare al’umma .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...