Daga Kwamaret Baffa B Shehu
Kowanne lokaci a Nigeria ana ta bata baiwa matasa damar shiga cikin sha’anin mulki shi zai taimaka wajen magance matsalolin da karar take fuskan.
Masu wannan raji sun tabbatar da cewa Matasa su suke da basira da kaifin tunanin abubunwan da ya kamata a bujiro da su wadanda za su ciyar da al’umma gaban.
A wannan karon zamu iya cewa Allah ya taimaki al’ummar karamar hukumar wudil domin sun sami Dantakara matashi wanda yake da Ilimi mai zurbi da kuma hangen nesan da zai kawo cigaba wanda duk dan karamar hukumar wudil zai yi alfahari da shi.
Hon. Abba Muhammad Tukur shi ne Dantakara shugaban karamar hukumar wudil a jam’iyyar NNPP kuma shi ne dan takara mafi kankantar shekaru cikin wadanda suka sami damar yin takarar shugaban karamar hukumar a jihar kano baki daya a zaɓen da za’a gudanar ranar 26 ga watan October mai zuwa.
Dan haka ya kamata mu san waye Hon. Abba Muhammad Tukur ‘
An haifi Hon. Abba Muhammad Tukur, a unguwar kofar fada dake cikin garin Utai a karamar Wudil ta jihar Kano a ranar 4 ga watan Maris, 1989.
Na Fara Cimma Burina na Farfado da Martabar Gidan Rediyon Jihar Kano – Abubakar Adamu Rano
malami, wakilin canji, dan siyasa, kuma mai fafutuka,
Ya yi karatun firamare a Utai Central Primary School a shekarar 2002. Bayan haka, ya halarci Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Sumaila, inda ya samu shaidar kammala karatunsa ta karamar Sakandire (JSSCE) a shekarar 2005.
Abba ya kammala karatunsa na babbar sakandire (SSCE) a Commercial School Wudil a shekarar 2008. Ya kuma shiga makarantar Sa’adatu rimi college of Education Kano, Inda ya yi NCE a fannin kasuwanci .
Bayan na ya yi B.Ed a fannin ilimin manya da cigaban al’umma, kuma ya yi Digiri na biyu a fannin Ilimin Manya da Ci gaban Al’umma, dukkansu daga Jami’ar Bayero Kano.
A yanzu haka yana karatun digirinsa na uku, wato PhD (in view) a fannin ilimin manya, inda ya kware a fannin ilimin manya a Jami’ar Bayero ta Kano. Yana da ƙwarewa a fannonin da ya karantawa da sauran fannonin ilimi, siyasa da zamantakewa, kuma ya ba da gudummawa sosai ga al’ummarsa musamman a fannonin da ya kware.
Kamar kowanne Yaro a kasar hausa, Hon. Abba Muhammad Tukur ya karatu al’qur’ani da sauran fannonin Addinin Musulunci kuma har yanzu bai tsaya ba.
Yanzu haka Honorabul Abba Muhammad Tukur shi jam’iyyar NNPP ta baiwa takarar kujerar shugaban karamar hukumar Wudil a zaɓen kananan hukumomi da za a gudanar ranar 26 ga watan October mai zuwa.
Muna addu’ar Allah ya bashi nasara ya kuma yi masa jagora”.