Kwalejin Sa’adatu Rimi: Tsohon kwamishinan ilimi zamanin Kwankwaso ya kalubalanci gwamnatin Kano

Date:

Daga Sani Danbala Gwarzo

 

Tsohon kwamishinan kasafi da tsatsare a gwamnatin data gabata, Ibrahim Dan Azumi Gwarzo ya ce dawo da Jami’ar Sa’adatu Rimi zuwa kwaleji da gwamnatin Kano ta yi daga koma baya ne ga daliban dake karatu a makarantar da kuma bangaran ilimi baki daya.

Dan Azumi Gwarzo ya ce makarantar ta cika duk wasu sharudda na zama jami’a duba da yadda hukumar kula da jami’o’i ta kasa ta tantance tare da bada shedar fara karatun digiri a makarantar.

Dan Azumi Gwarzo wanda ya taba zama kwamishinan ilimi a zangon farko na mulkin Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da wakilin kadaura24.

Ganduje ya musanta kitsa yadda za’a sake tsige sarki Sunusi II

” Wannan matakin Bai da ce ace gwamnatin da take ikirarin mai ilimi muhimmanci ce ta yanke shi ba, domin ya nuna karara cewa gwamnatin kawai adawar Siyasa take ba maganar cigaban al’ummar jihar Kano ba”.

Takutaha: Mu dage da addu’ar neman sauki a wajen Allah kan halin da Nigeria take ciki – Falakin Shinkafi ga Musulmi

Ya ce gwamnatin ganduje ta yi duk mai yiwuwa wajen samar da gine-gine da kayan aiki da tallafawa makarantar ta zama jami’a da dalibai zasu rika karatun digiri mai makon samun shaidar koyarwa ta N.C.E.

Tsohon kwamishinan ya ce gwamnatin kano bata shiryawa bangaran ilimin ba domin ba gaske take ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Nan gaba kadan za mu bayyana sunayen masu ɗaukar nauyin ta’addanci a Najeriya – Babban Hafsan tsaro

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce...

Wasu yan daba sun ajiye Makamansu a Kano

Gwamnatin Jihar Kano Hadin gwaiwa da Rundunar Yansandan Jihar...

Masu Mukamai a gwamnatin Kano ba su da uzurin kin taimakawa yan Kwankwasiyya – Sanusi Bature

Mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin...

Magoya bayan Barr Ibrahim Isa (Matawallen Gwagwarwa) sun aikawa Gwamnan Kano Budaddiyar Wasika

Daga Isa Ahmad Getso Kira don nemawa Barr. Ibrahim Isa...