Zaben Ƙato bayan Ƙato: Gwamnonin APC sun nemi Malami ya hana Buhari sanya hannu a dokar zabe

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusfu
 Gwamnonin jam’iyyar APC sun fara tuntubar ministan shari’a, Abubakar Malami (SAN), da nufin ya shawo kan shugaban kasa, Muhammadu Buhari yaƙi amincewa da dokar zaɓe da aka yiwa gyara wadda majalisar dokokin kasar ƙasa ta zartar a ranar Talatar data gabata.
 Gwamnonin APC na karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu.  Shi ma Malami dan jihar Kebbi ne kuma ana ta rade-radin za’a baiwa Malamin takarar gwamna kebbin a 2023.
 Wani hadimi ga daya daga cikin gwamnonin APC ya shaidawa jaridar PUNCH cewa kamar sauran kudirorin da aka mika wa shugaban kasa, ana sa ran Buhari zai mika wa Malami kudirin dokar zabe domin neman shawararsa ta fuskar doka.
Dama dai an dade ana ta cece-kuce akan batun sabuwar dokar wadda ake ganin bazata yiwa gwamnonin daɗi ba ,shi yasa suke ta sukar dokar tare da bin duk wata hanya da za su kawo naƙasu ga dokar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...