Daga Rahama Umar Kwaru
Guda cikin Mata yan jaridu a Kano mai suna Rukayya Umar ta koka da yadda kwamitin dake Shirya zaben kungiyar mata yan jaridu ta kasa reshen jihar kano ke gudanar da aikinsa .
Rukayya Umar ta rubuta koken nata ne zuwa ga uwar kungiyar yan jaridu ta kasa, Sannan ta tura kwafin takardar ga kwamishinan yada labarai na jihar kano da kwamishinan yan sanda na kano da Shugabar NAWOJ ta kasa da sauran masu ruwa da tsaki.
A cikin wasikar Rukayya Umar ta yi zarge-zarge har guda hudu da take bukatar uwar kungiyar yan jaridu ta kasa NUJ ta gaggauta daukar mataki akan batun domin tabbatar da Adalci ga koya.
“Na rubutu wannan wasikar ne domin nuna matukar damuwa dangane da yadda kwamitin zaben da aka nada domin sa ido kan zaben kungiyar mata ‘yan jarida ta Najeriya (NAWOJ), reshen Kano. Mun yi imanin cewa batutuwan da aka zayyana a ƙasa suna buƙatar kulawa ta gaggawa”.
Batutuwan su ne kamar haka ;
1. Batun Shugabar Kwamitin: Shugabar Kwamitin Zabe ba mamba ba ce ta NUJ ko NAWOJ, kamar yadda yake bisa dolar duk wani ma’aikacin National Orientation Agency (NOA), ba mamba ba ne na NUJ. Kuma wacce aka baiwa shugabancin kwamitin ma’aikaciya ce a hukumar ta NOA don haka muke ganin hakan zai shafi sahihancin zaben, indai ita ce zata jagoranci kwamitin .
2. Kudaden Fom shiga Zaɓen: Kwamitin Zabe ya sanya kudaden masu yawa a matsayin kudaden fom na yin fom din yin takara wanda muke ganin hakan bai da ce ba. An sa kudin Fom din takarar kujerar shugaban kungiyar NAWOJ Kano akan kudi naira dubu dari, yayin da fom din kujera mafi kankanta ya kai naira dubu sittin. Hakan dai ya bambanta da zaben NUJ reshen jihar Kano da aka gudanar a kwanan baya, inda aka cimma matsaya, aka sayar da fom din takarar kujerar shugaba a kan naira dubu sittin, kujera mafi kankanta kuma naira dubu talatin. Irin wadannan makudan kudade da kwamitin ya sanya na iya hana masu neman tsayawa takara shiga zaben.
An Karrama Mai Magana Da Yawun Gwamnan Kano Kan Batun Taimakawa Daliban Dawaki Tofa
3.Fargaba kan ‘Yan Kwamitin Zaɓen: Akwai fargabar cewa wasu daga cikin ‘yan kwamitin zaben na nuna kyama ga wasu mutane da suka nuna sha’awar tsayawa takara a mukamai daban-daban. Wannan son zuciya zai iya kawo cikas wajen yin adalci ga kowa .
4. Yin watsi da Sharuɗɗan Cancantar Masu takara: Mun lura cewa kwamitin zaɓe zai yi watsi da wasu sharuɗɗan cancantar masu takara. Wannan rashin bin ka’idojin da aka samar zai iya haifar da zaben ‘yan takarar da ba su cika sharuddan da suka dace ba, wanda hakan zai kara kawo cikas ga ingancin zaben.
Ta ce “Bisa la’akari da waɗannan manyan abubuwan da ke damun mu, cikin girmamawa muna neman daukin kungiyar NUJ ta ƙasa, wanda NAWOJ ke karkashin ta domin tabbatar da daukar matakin da ya dace don yin Adalci ga kowa .