Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Kungiyar APC Media Forum Gawuna/ Garo ta jihar kano, dake tallata manufofin jam’iyyar APC a gidajen Radio ta dakatar da aikin kare mutuncin jam’iyyar da kuma shugabanni da jagororin jam’iyyar ba tare da bata lokaci ba.
” Daga yau juma’a 16 ga watan Ugusta 2024, muna umartar dukkanin ya’yan wannan kungiya da su tsaya chak da kare mutuncin jam’iyyar APC ko wani jagora a cikin ta har sai mun dawo mun ce muku ku cigaba”.
Shugaban kungiyar Aminu Black Gwale ne ya bayyana hakan cikin wani sautin muryarsa da aka turowa Kadaura24 a ranar juma’ar nan.
Ya ca ba za su cigaba da kare muhibbar jam’iyyar da jagoransu ba, har sai an warware matsalolin da suka addabe su, wadanda suka ce ana yi musu Abubuwa wadanda ba sa jin dadinsu.
Babban Hadimin Gwamnan Kano ya ajiye Mukaminsa tare da Komawa APC
Aminu Black Gwale ya ce sun dauki wannan matakin ne bayan da su shugabannin kungiyar suka zauna Sannan suka cimma matsaya, don haka ya ce suna umartar dukkanin ya’yan kungiyar dake ƙananan hukumomi 44 da su dakatar da kare muhibbar jam’iyyar APC.
“Ana tauye mana hakkokinmu, ba a tausaya mana, don haka mun dakatar da aikin da muke, tunda dai ba wanda bai san wahalar da muka sha ba, amma yanzu an yi watsi da mu, to mu ma Mun dakata har sai an gyra sai mu dawo”. Inji black gwale
Dalilin da ya sa kotu ta mikawa kamfanin China jiragen Shugaban ƙasar Nigeria
A yan Kwanakin nan dai jam’iyyar APC musamman a Kano tana fama da yan matsalolin nan da can wadanda kuma idan shugabannin jam’iyyar ba su tashi tsaye ba, za su iya fuskantar zaizayar magoya baya.