Babban Hadimin Gwamnan Kano ya ajiye Mukaminsa tare da Komawa APC

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

Guda cikin masu taimakawa gwamnan jihar kano na musamman Abdulrahman Muhammad Sulaiman wanda aka fi sani da Mai-Kadama, ya ajiye mukaminsa tare da ficewa daga jam’iyyar NNPP.

Mai-Kadama ya fice daga jam’iyyar NNPP ne zuwa jam’iyyar APC.

Dan siyasar wanda shi ne SSA ga gwamnan kan harkokin sana’o’i, ya bayyana sauya shekarsa ne a ranar Laraba a Abuja, bayan wata ganawa da sanata Barau Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Sace takardun Shari’a : Ganduje ya yiwa gwamnatin Kano martani

Mai-Kadama ya rike mukamai da dama kafin ya sauya sheka, ciki har da jagorantar tafiyar Kwankwasiyya a jihar Filato.

Hakazalika, ya kasance shugaban kungiyar G-6 a jihar Kano.

Mai-kadama tare da Sanata Barau Jibril

A wani sako da ya wallafa a Facebook, Barau Jibrin ya ce Mai-Kadama ya koma jam’iyyar APC ne domin samun shugabanci nagari da kuma habaka ci gaba.

Sanarwar ta kara da cewa, ” jam’iyyar APC ta sami karuwa domin wani babban jigon jam’iyyar NNPP, da kuma tafiyar Kwankwasiyya, Abdulrahman Mai Kadama wankwasiyya ya koma jam’iyyarmu,” in ji sanarwar.

An ƙayyade kuɗin fom din tsayawa takara a zaɓen ƙananan hukumomin Kano

“Yau na karɓi bakuncin Mai Kadama Kwankwasiyya a gidana da ke Abuja, inda ya jefar da jar hula ya koma babbar jam’iyyar siyasa a Afirka, APC.

“Da ya sauya shekar zuwa jam’iyyar APC ya bayyana cewa shi ne Mai Kadama Maliya. Dan siyasar ya kuma bayyana yin murabus daga mukaminsa na babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kano kan harkokin sana’o’i II.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi: Kawu Sumaila ya jinjinawa Gwamnan Kano

Sanatan da ke wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar...

Gwamna Yusuf Ya Shirya Baiwa Kananan Hukumomin Kano Cikakken ‘Yan cin Kai

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince...

Majalisar Zartarwa ta jihar Kano ta Amince da kashe Naira Biliyan 18 don aiwatar da wasu aiyuka

  Majalisar zartarwar jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir...

Gwamnatin Kano ta nemi majalisar dokokin jihar ta haramta auren jinsi

Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci majalisar dokokin jihar ta...