Yanzu-Yanzu: Ganduje ya Sanyawa dokar Kasuwar Kantin kwari hannu tare da Wasu dokokin

Date:

Daga Zainab Muhd Darmanawa

 

Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Sanya hannu a dokoki guda 3 Waɗanda Majalisar dokokin Jihar Kano ta zartar da su.

Gwamnan ya Sanya hannu ne yayin taron Majalisar Zartarwar wannna makon, Wanda ya gudana Gidan Gwamnatin Kano.

Jim kadan bayan kammala Sanya Hannu akan Dokokin Wanda Suka kunshi dokar Kasuwar Kantin kwari da kuma ta dokar C P C da aka yiwa kwaskwarima sai Kuma dokar ta Hukumar kula da yawon bude idanu da itama akai Ma ta kwaskwarima.

Dangane da sabuwar dokar Kasuwar Kantin kwari Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya ce anyi dokar ne Saboda a Kara gyautata al’amuran Kasuwar da Kuma yadda Gwamnati zata Rika Samun kudaden haraji a Kasuwar.

Yace ya Zama wajibi Gwamnati yi dokar Saboda yadda ta Kashe makudan kudade wajen gyaran Kasuwar da Kuma yadda Wasu Yan Kasuwar suke so su Rika bijirewa Gwamnati.

“Wasu Ƙungiyoyi a Kasuwar Suna ganin sun yi karfin da Gwamnati ba zata iya juya su ba, to Amma da Wannan dokar Insha Allah komai Zai tafi yadda ake bukata”. Inji Ganduje

Game da Sauran dokokin kuwa Gwamna Ganduje yace an yi musu gyarane Saboda akwai bukatar hakan don gyautata aiyukan Hukumominsu biyu.

” Dokar CPC zata Kara baiwa al’umma damar su Shigo su bada Gudunmawar su a duk Wani Aikin cigaba da Gwamnati zata gudanar, summan a bangare Ilimi lafiya da dai Sauransu”. Inji Gwamnan

Taron Majalisar Zartarwar na wannna makon ya samu halartar dukkanin ya’yan Majalisar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnan Kano ya gabatar da kasafin kudin 2026 da ya kai N1.368 tiriliyan

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar...

Nazarin Yadda Shaharar Sanata Barau Ta Karade Nigeria – Abba Anwar

Daga Abba Anwar Wani babban abin lura game da rayuwar...

Kungiyar Ɗaliban Mariri ta gudanar da aikin duba marasa Lafiya kyauta a yankin

Daga Abdallahi Shu'aibu Hayewa   Kungiyar Dalibai ta Makarantar Mariri wato...

Gwamnan Taraba ya bayyana dalilinsa na shirin komawa APC

Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya ce zai shiga...