Daga Halima Musa Sabaru
Gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC mai mulki a Nigeria sun ce basu san dalilin da yasa ake shirin, gudanar da zanga-zanga ba a kasar.
Shugaban kungiyar gwamnonin wanda kuma shi gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ne ya bayyana haka lokacin da yake jawabi bayan wani taron nkungiyar gwamnoni Progressives’ Governors Forum (PGF) da aka gudanar a Abuja,in da yace ba mu san masu shirya zanga-zangar me suke shirin yi ba, muna kira da su zo muzauna a tattauna domin samun mafita.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta ruwaito cewa wasu mutane na yin gangamin shirya zanga-zangar da za a yi a fadin kasar daga ranar 1 ga Agusta zuwa 10 ga Agusta, 2024.
Sauyin Yanayi: Za mu fara daukar tsauraran matakai akan masu sare itatuwa barkatai -Gwamnan Kano
“Mu a matsayinmu mun himmatu wajen tabbatar da hadin kan kasar nan, mun himmatu ga duk wani abu da zai inganta rayuwar ‘yan Nijeriya, ya kawo wadata, samar da ayyukan yi ga matasa maza da mata wadanda suka kammala karatunsu domin a samar musu aiki yi”. A cewar Uzodimma
Gwamnan Uzodimma ya ci gaba da cewa bai dace a halin yanzu kasar nan ta yi wata zanga-zangar da wata kungiya za ta yi ba, inda ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da wannan zanga-zangar.
Ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su yi hakuri da gwamnati, yana mai cewa ana ci gaba da kokarin ganin an daidaita matsalar tattalin arzikin da ake fama da ita a kasar.
ya kara da cewa: “Muna ganin ba hikima ba ne a halin yanzu a yi duk wata zanga-zanga”.
Muna amfani da wannan dama don mu shawarci matasan mu maza da mata da su daina bari ana tunzura su har a haddasa rikici ko hargitsi a kasar nan.
Daily Trust