Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya tare da yin alkawarin sake duba dokar mafi karancin albashi ta kasa duk bayan shekara uku.
Shugaba Tinubu ya kuma yi alkawarin samar da hanyoyin da za su taimaka wa kamfanoni masu zaman kansu da na kananan hukumomi wajen biyan mafi karancin albashin.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a taron da ya yi da shugabannin TUC da NLC ranar Alhamis a Abuja, wanda shi ne karo na biyu da bangarorin suka gana cikin kwanaki 7.
Majalisar wakilci ta dauki matakin don magance tsadar kayan abinchi a Nigeria
Shugabannin kungiyar kwadagon sun yabawa shugaba Tinubu kan wannan mataki da ya dauka, shugaban kasar ya kuma yi alkawarin yin amfani da karfin ikonsa wajen biyan bukatun kungiyoyin jami’o’in na neman albashin watanni 4 ba a biya su ba.