Sabuwar shekara: Minista Gwarzo ya taya al’ummar Musulmi Murna

Date:

 

Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane, Abdullahi Tijjani Gwarzo ya taya al’ummar Musulmin Najeriya murnar shiga sabuwar shekarr Musulunci ta 1446 bayan Hijira.

Minista Gwarzo ya ce wannan lokaci da watan Muharram lokaci ne da yake da matukar muhimmaci ga Musulmi don haka ya bukaci al’ummar Nigeria da su hada kawunansu don samu cigaba mai dorewa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga karamin ministan kan harkokin yada labarai Adamu Abdullahi ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.

Talla

Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da yin abubuwan alkhairin da suka faro tun a shekarar da ta gabata, sannan su yi amfani da wannan dama wajen yin addu’o’i domin samun zaman lafiya da ci gaba a kasar nan tare da bayar da goyon baya ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu na kokarinsa na kyautata rayuwar ‘yan kasa.

Don haka Gwarzo ya jaddada bukatar ‘yan Najeriya su hada hannu wuri guda, ba tare da bambancin addini ko kabila ba, yana mai cewa yin hakan shi ne ginshikin ciyar da kasa gaba.

Rikicin masarautar Kano: Abun da ya faru a zaman kotu na yau talata

“Ci gabanmu ya ta’allaka ne da yadda muke aiwatar da koyarwar addinin Musulunci, wadda ke koyar da ‘yan Adam yadda za su zauna da juna lafiya,” in ji Gwarzo, ya kara da cewa “yanzu mun shigo sabuwar shekarar Musulunci, ya zama wajibi ga dukkan Musulmin Nijeriya su rika gudanar da aiki bisa ka’idojin Musulunci don ci gaban kasarmu.”

Don haka Ministan ya yabawa Musulman Najeriya bisa yadda suke nuna biyayya da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban dimokuradiyyar kasar nan. Ya bayyana cewa sabuwar shekarar Musulunci za ta kasance cikin wadata domin ‘yan Najeriya za su sami alkhairai da damammaki a wannan shekara .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...