Tsadar Rayuwa: Kar ku biye wa masu son yin zanga-zanga a Kano – Amb. Ibrahim Waiya

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Kwamitin zaman lafiya na jihar kano ya yi kira ga al’ummar jihar da su guji shiga zanga-zangar yanayin tsadar rayuwa da ake ciki a kano kamar yadda wata majiya mai ƙarfi ta bayyana cewa ana shirin yin zanga-zangar.

Majiyar tace wasu muggan mutane sun shirya tsaf domin gudanar da zanga-zangar a jihar Kano.

Rikicin Masarauta: An Samu Tsaiko A Shari’ar Sarautar Kano

Shugaban sakatariyar kwamitin zaman lafiya na jihar Kano kuma shugaban kungiyoyin fararen hula na jihar Kano, Amb. Ibrahim Waiya ne ya bayyana hakan a wani saƙon murya da ya aikowa kadaura24.

Ya bayyana cewa jihar Kano ita ce jiha ɗaya tilo da arewacin najeriya ke alfahari da ita wajen samar da zaman lafiya, wanda hakan ne yasa jihar ta yi fice a harkokin kasuwanci na yau da kullum a ƙasa dama nahiyar Afirka gaba ɗaya .

Gwamnatin Kano ta tasamma warware rikicin ta da yan jaridun da sukai Mata tawaye

Amb. Ibrahim Waiya ya ce yanayin ƙuncin rayuwa da ake ciki kamata ya yi al’umma su koma ga Allah domin neman sauƙi kamar yadda aka duƙufa lokacin watan azumin Ramadana.

Waiya ya ƙara da cewa ya kamata al’umma su zama masu kishin jihar su domin ba su da jihar da ta fi ta a yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Likitocin Jinya da Ungozoma sun janye yajin aiki – Ministan lafiya

Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Ƙasa (NANNM) ta...

Sarkin Hausawan Arewa, Amb. Balarabe Tatari, Ya Aike da Sakon Ta’aziyyar Buhari da Dantata

Sarkin Hausawan Arewa kuma Ambasadan Zaman Lafiya, Alhaji Balarabe...

INEC ta sanya ranar fara rijistar masu zabe a Nigeria

Hukumar zaɓen Najeriya ta ce nan gaba cikin wannan...