Daga Halima M Abubakar
Al’ummar Jihar kogi sun shaida salon jagoranci iri -iri, amma Wasu yan jihar sun Shaidawa Jaridar kanodaily cewa ba su ta taɓa ganin Gwarzon Gwamna, mai son zaman lafiya da son cigaban al’ummar ba kamar Gwamna Yahaya Bello ba.
Babu shakka Gwamnan al’ummar ya fuskanci Kalubale Mai tarin yawa, daga Yan hamayya na Cikin gida da waje, amma duk da waɗannan ƙalubalen Gwamnan sai da ya kau da Kansa ya cigaba da gudanar da aiyukan raya Kasa don mai da jihar Kogi ƙaramar Dubai.
Abin da yawancin ‘yan Najeriya ba za su taɓa sani ba game da Gwamna Yahaya Bello shi ne, manyan nasarorin da ya samu a jihar Kogi wanda ya fara kammala da ayyukan da aka faro a yankuna da dama na jihar.
An rubuta cewa jihar Kogi tana daya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Arewa ta Tsakiya, mutanen jihar kogi suna bacci da idanun biyu, ”bisa ga dacewa da dabarun tsaro da Gwamna Bello ya Kawo a Matsayin sa na babban jami’in tsaro na jihar Kogi.
Idan za a iya tunawa bayan an rantsar da Gwamna Yahaya Bello ya karbi ragamar jagorancin jihar Kogi a shekarar 2016, Bello ya ayyana Kudirinsa na yaki da ‘yan fashi da makami da masu aikata laifuka da dama da ke aiki a jihar.
Don cimma wannan manufa, Yahaya Bello ya yaki Masu adawa garkuwa da mutane a jihar waɗanda ake ganin kamar baza su tabu ba. Ya rusa gine -ginen su na zama da maboyar su inda ba a Bai taba barin ayyukan muggan ayyuka ba.
Wannan gagarumin yunƙurin ya fitar da jihar Kogi daga barazanar garkuwa da mutane, ayyukan masu asiri, da rikicin kabilanci tsakanin al’umma.
Matashin Gwamnan a koyaushe Idan Zai fito da Wani al’amari daya Shafi rayuwar al’ummar kogi baya yi kai tsaye sai ya tuntubi masana a fannin da Sauran Masu Ruwa da tsaki don tabbatar da Cewa an yi abun da al’umma zasu Amfana komai daren dadewa.
Babu shakka Alhaji Yahaya Bello shine irin jagoran da Najeriya ke nema, domin yana da gogewa, jajircewa, himma, tabbas idan aka ba shi dama zai ciyar da Ƙasar nan gaba.
A wannan lokacin bari in lissafa wasu manyan ayyukan da Mai kishin Al’umma, Gwamna Yahaya Bello ya aiwatar a jihar Kogi, wanda suke nuna karara cewa idan ya hau kurar Shugabancin Najeriya, ‘yan Najeriya za su ji dadi kuma za su Shaida aiyukan raya Kasa da bunkasa Rayuwar al’umma.
Da farko, Gwamna Yahaya Bello ya gina tare da kaddamar da Gidan Hadin Kan Igala a Anyigba kuma ya buɗe shi a watan Yuli 2019 Inda manyan jami’an gwamnati da dama suka halarta.
Manufar wannan aikin ita ce hada kan ‘yan jihar Kogi, ba tare da la’akari da bambancin kabila ko addini ba.
A yunƙurinsa na samar da ƙarin kuɗaɗe don jihar don gudanar da manyan ayyuka a Jihar, Yahaya Bello ya gina Babban ofishin karɓar haraji na farko a Lokoja kuma ya taimaka wajen sami da Karin kudaden haraji a Jihar.
Yahaya Bello ya ci gaba da farawa tare da kammala masana’antar sarrafa shinkafa ta Kogi ta farko a Ejiba, cikin ƙaramar hukumar Yagba ta yamma a jihar Kogi.
Za a lissafa ƙarin nasarorin Gwamna Yahaya Bello a cikin wallafe -wallafen mu.