Kedco sun bukaci Jama’a su rika biyan cikakkun kudin wutar lantarki

Date:

Daga Nura Abubakar
 Hukumar gudanarwar Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) ya bukaci abokan huldar su a Jihohin Kano, Katsina da Jigawa da su rungumi dabi’ar biyan kuɗin wutar lantarki .
 Cikin Wata Sanarwa da Shugaban Sashin hulɗa da Jama’a na kamfanin Ibrahim Sani Shawai ya aikowa Kadaura24 yace hukumar gudanarwar tace biyan cikakkun kudin watar zai taimaka wa kamfanin ya ci gaba da ƙoƙarin da yake na samar da ingantacciyar Wutar lantarki.
 Batun sashi biyan kuɗin wuta kuwa wanda kusan ya zama ruwan dare, hakan yana kawowa ayyukan KEDCO na gamsar da sauran abokan hulɗa da Wutar lantarki.
 Abokan cinikinmu yakamata su fahimci cewa hanya ɗaya da za su ƙarfafa gwiwar KEDCO don haɓaka samar da wutar lantarki shi ne su Rika biyan Kamfanin kudin da aka rubutu musu yadda ya kamata.
Sanarwar tace suna rokon abokan ciniki su zasu fahimce su yadda ya dace domin basu damar sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...

Rasuwar Aminu Ɗantata babban rashi ne ga Duniya baki daya – Shugaban kamfanin Yahuza Suya

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Shugaban kamfanin Yahuza Suya & Catering...