Daga Halima M Abubakar
Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje yace ba shi bane ya kirawa ayarin su Malam Ibrahim Shekarau a Matsayin Banzan bakwai ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne Cikin Wata Maganawa da sukai da Sashin Hausa na Radio Faransa.
Ganduje yace Wani ne ya tambayi Cewa Wadancan da basa tare da Gwamnati su nawa ne? sai aka ce Masa su Bakwai ne ,to shi ne ya kirawo su da Sunan Banza bakwai.
” Gwamna bai cewa kowa banza bakwai wani ne ya fada ,Amma ba ni ba” inji Ganduje
Da aka tambaye shi ko zasu bude Kofar sulhu da su Malam Ibrahim Shekarau ?
Ganduje yace Kofa abude take za’a nemi su Wadancan Sanatoci guda 2 da Yan Majalisu 4 da suke ganin ba’a kyuata musu a APC domin aga ta hanayar da za’a warware Matsalolin don a tafi tare gaba daya.
Kadaura24 ta rawaito Rikicin cikin gida ya barke tsakanin Tsohon Gwamnan Kano Kuma Sanatan Kano ta tsaki Malam Ibrahim Shekarau da wasu Yan Majalisu Saboda abun da suka kirawa Rashin adalci da ake yi musu har Suka Kai Kara ga uwar jam’iyyar APC ta Kasa.
Sha Sha Sha kawai