Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa za ta inganta walwala da kuma yanayin aiki ga ma’aikata a jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin bikin ranar ma’aikata ta duniya da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha Kano.
Gwamnan wanda mataimakinsa Alhaji Aminu Abdulsalam Gwarzo ya wakilta, ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an biya ma’aikatan da suka yi ritaya hakkokin su a kan lokaci da kuma kudaden fansho domin inganta rayuwarsu.
Ya kuma yi nuni da cewa, ana shirin kaddamar da tsarin da ya dace na samar da gidaje ga ma’aikata, yana mai jaddada cewa idan aka kaddamar da shirin zai bai wa ma’aikata damar mallakar gidaje a farashi mai rahusa.
Kungiyar Kwadago ta yi fatali da karin albashin da Tinubu ya yiwa ma’aikatan Nigeria
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ci gaba da cewa gwamnatinsa ta ba da fifiko wajen bunkasa ilimi, noma, da samar da lafiya da dai sauransu.
Ya kuma yi kira ga ma’aikatan jihar Kano da su sakawa gwamnatin ta hanyar jajircewa da sadaukarwa a wajen aiyukan su.
Tinubu ya karawa ma’aikatan Nigeria albashi
A nasa jawabin, shugaban kungiyar Kwadago ta kasa reshen jihar Kano, Kwamared Kabiru Inuwa ya taya gwamna Yusuf murnar samun nasara a shari’ar da aka yi a kotu.
Ya zayyana wasu daga cikin nasarorin da Gwamna Yusuf ya samu karkashin gwamnatin sa kamar
biyan albashi a kan lokaci, cikakken biyan fansho ba tare da yanke musu komai ba, dawo da biyan albashi ga Ma’aikatan da gwamnatin da ta gabata ta dauka aiki bayan zaben 2023.
Sauran sun hada da biyan hakkokin wadanda suka yi ritaya da na wadanda suka mutu da daukar nauyin ma’aikata zuwa jami’o’in kasashen waje domin neman ilimi.