Kungiyar Kwadago ta yi fatali da karin albashin da Tinubu ya yiwa ma’aikatan Nigeria

Date:

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta yi watsi da karin albashin da Gwamnatin Tarayya tayi musu a masayin “bata lokaci.”

Kadaura24 ta ruwaito a daren Talata cewa gwamnatin ta yi wa ma’aikatanta karin kashi 25 zuwa 35 na albashinsu; ’yan fansho kuma kashi 20 zuwa kashi 28.

Sanarwar da mai magana da yawun hukumar kula da albashi ta kasa (NSIWC), Emmanuel Njoku, ya fitar ta duk karin za su fara aiki ne daga watan Janairun 2024.

Tinubu ya karawa ma’aikatan Nigeria albashi

Njoku ya kuma shaida wa Aminiya cewa za a biya ma’aikatan cikon karin albashin na watannin da suka gabata.

Sanarwar karin ta fito ne sa’o’i kadan kafin Ranar Ma’aikata ta Duniya, wanda hakan ya sa ake ganin karin wani albishir ne ga ma’aikatan gwamnati.

Kazalik karin albashin da aka yi, yana daga cikin shawarwarin kwamitin mutum 37 daga gwamnati da yan kwadago da sauran masu ruwa da tsaki da gwamnati ta kafa kan karin albashi, karjashin jagorancin tsohon shugaban ma’aikata, Bukar Goni Aji, a watan Janairu.

Ma’aikatan da aka yi wa karin albashi sun hada da masu karbar albashi na bai-daya, wato Consolidated.

 

Wannan karin albashi na zuwa ne a jajabirin bikin Ranar Ma’aikata ta Duniya ta bana.

Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) dai ta dade tana neman a yi wa ma’aikata karin albashi, bisa la’akari da yadda abubuwan masarufi suka yi tashin gwauron zabo a ƙasar tun bayan da gwamnati ta sanar da janye tallafin mai a ranar 29 ga Mayu, 2023 da aka rantsar da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu.

Aminiya ta ruwaito cewa kungiyar ma’aikatan jami’a ta bayyana cewa mambobinta ba za su amince da mafi ƙarancin albashin da ya faza Naira dubu 300 ba.

Sai dai duk da cewa wakilinmu na samun karin bayani, jami’in na NLC ya ki kara cewa komai kan lamarin.

Mun yi kokarin samun karin bayani daga wasu manyan jami’an NLC da takwarorinsu na kungiyar ma’aikata (TUC) amma hakan bai samu ba a daren.

NLC da sauran kungiyoyin kwadago dai na kira ne da a sanya mafi karancin albashi ya zama wanda zai wadaci ma’aikaci, gwargwadon yanayin tsadar rayuwa a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-Yanzu: An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana'izar fitaccen ɗankasuwar...

Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika sakon ta’aziyyar Rasuwar Aminu Dantata

Daga Sadiya Ahmad   Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika...

Kungiyar ’Yan Jaridun Kano Arewa ta Aike da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Alhaji Aminu Dantata

  Kungiyar ’Yan Jarida ta Kano Arewa ta bayyana alhinin...

Ku na da rawar takawa wajen inganta Lafiyar al’ummar Kano – Waiya ga jami’an yada labarai

Daga Abubakar Sayeed Kwamishinan Ma'aikatar yada labarai da harkokin cikin...