Gwamnatin tarayya a Najeriya ta yi wa ma’aikatanta ƙarin albashi da kimanin kashi 25 cikin ɗari zuwa kashi 35 cikin ɗari.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake gudanar d bikin ranar ma’aikata ta duniya.
A ranar Talata ne wata takarda daga shugaban hukumar kula da albashi ta Najeriya, Ekpo Nta ta tabbatar da ƙarin albashin.
Takardar ta nuna cewa ƙarin albashin zai fara ne daga ranar ɗaya ga watan Janairun 2024.
Da dumi-dumi: NNPC ya sanar da ranar da Zai kawo karshen ƙarancin man fetur a Nigeria
Kamar akasarin al’umma ƙasar, ma’aikatan gwamnati a Najeriya sun faɗa cikin mawuyacin hali sanadiyyar matsin tattalin arziƙi.
Kayan masarufi sun yi tashin gwauron zabi sannan darajar naira ta zube idan aka kwatanta da dalar Amurka duk kuwa da sabbin matakan da gwamnatin ƙasar ke ci gaba da ɗauka.
Yanzu haka akwai wani kwamiti da gwamnatin ƙasar ta kafa wanda ke aiki tare da ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasar domin samar da matsaya kan ƙarancin albashi ga ma’aikata a ƙasar.
A baya ƙungiyoyin ƙwadago sun sha yin barazanar shiga yajin aiki da durƙusar da lamurra a ƙasar domin tursasa wa gwamnatin tarayya ɗaukan matakan bunƙasa walwalar ma’aikata.
Kotu ta sanya ranar fara sauraron Shari’ar Ganduje kan korar shi daga APC
A halin yanzu mafi ƙarncin albashin ma’aikata a hukumance shi ne naira 30,000.
Kuma duk da haka akasarin gwamnatocin jihohi ba su iya biyan ma’aikatansu albashin mafi ƙaranci, inda akan samu wasu ma’aikata na bin bashin albashin watanni da dama.
Wannan sabon albashin da gwamnatin ta amince da shi zai shafi ma’aikatan gwamnati da ke bisa tsarin CONPSS, da na ma’aikatan kwalejojin bincike na CONRAISS, da jami’an ƴansanda (CONPOSS) da ma’aikatan tattara bayanan sirri (CONICCS) da sauran masu ɗamara (CONPASS) da kuma dakarun ƙasar (CONAFSS).