Daga Nura Abubakar Bichi
Kwamishinan Raya karkara da cigaban al’umma na Jihar Kano Hon. Musa Iliyasu kwankwaso ya bayyana cewa duk yadda Gwamna Abdullahi Ganduje ya dama Haka za’a Sha a Kano.
Musa Iliyasu kwankwaso ya bayyana hakan a taron Masu Ruwa da tsaki da Gwamna Ganduje ya kirawo a nan domin tattaunawa Kan al’amuran da suka Shafi jam’iyyar APC.
Musa Iliyasu yace Yanzu Abdullahi Umar Ganduje ne Gwamnan Kano Kuma ya Zama wajibi kowa ya bi duk wani abun daya fito dashi in dai a Kano ne.
” A Wannan dakin taro Kabiru Gaya yayi abun da yake so Kwankwaso yayi ,shima Malam Ibrahim Shekaraun yayi yadda yake so, to shima Ganduje tunda shi ne Gwamnan Kano dole abi abun da yace.” Inji Musa Kwankwaso
Kadaura24 ta rawaito Cewa a baya dai Musa Iliyasu kwankwaso ya yiwa Malam Ibrahim Shekarau Kwamishina Lokacin Yana Gwamnan Kano.