Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Jami’an tsaro na musamman da ke kula da Masallacin Harami da ke Makkah sun fara gudanar da bincike a kan wani mutum da ya fado daga benen saman masallacin.
Kadaura24 ta rawaito An kai mutumin asibiti domin ya sami kulawar da ta dace ba tare da bayyana ko Dan wacce kasa ce ba.
Ka Yi Aikin Dake Gabanka Ka Rabu Da Ganduje – Kwankwaso Ya Fadawa Abba Gida-gida
Rundunar ta musamman mai kula da tsaron masallacin Al Haram ta bayyana a shafinta na “X” wato Twitter cewa “an kammala duk abubunwan da suka dace,” ba tare da bayyana karin bayani kan lamarin ba.
Yanzu-yanzu: Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi sabbin nade-nade a Kano
Idan za’a iya tunawa a shekarar 2018, wani mahajjaci mai shekaru 26 ya kashe kansa a Masallacin Harami, lamarin da ya haifar da firgici da fargaba a tsakanin alhazai da masu ibada a Masallacin.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Makkah ta kafafen yada labarai ya bayyana a watan Yunin 2018 cewa jami’an tsaro sun fara gudanar da bincike kan lamarin inda wani mahajjaci ya fado da baya daga rufin Mas’a zuwa farfajiyar kasa, lamarin da ya yi sanadin rasa rayuka a bayan Maqam.