Daga Kamal Yahaya Zakaria
Gwamnatin tarayyar Nigeria ta amince da ranar Alhamis 11 ga watan Afrilu, 2024 a matsayin karin hutun domin murnar sallar karama ta bana.
Kadaura24 ta rawaito hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakatare a ma’aikatar harkokin cikin gida, Dr Aishetu Gogo Ndayako ya sanyawa hannu kuma aka raba wa manema labarai, ranar Talata.
Yanzu-yanzu: Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi sabbin nade-nade a Kano
Sanarwar tace ministan harkokin cikin gida Dr Olubunmi Tunji Ojo ya taya al’ummar musulmi murnar kammala Azumin watan Ramadana lafiya Tari da fatan musulmi zasu yi koyi da darussan da suka koya a cikin watan.
Kungiyar Yan Chanji Ta WAPA A Kano Ta Magantu Kan Karyewar Farashin Dala
Ya sake nanata kudurin Shugaba Bola Tinubu (GCFR) na tabbatar da samar da lafiya da wadata a Najeriya domin kowa ci gaba ga kowa.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa gwamnatin tarayya ta ware ranakun talata da Laraba a matsayin ranakun hutun karamar Sallah, sai dai an sami Karin ne sakamakon azumi 30 da Musulmi zasu Cika, Inda zasu gudanar da sallah a gobe Laraba saboda rashin ganin jinjirin watan Shawwal.