Muna da burin hada kan kasashen ECOWAS – Barau Jibril

Date:

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya ce suna da kuduri na ganin sun haɗa kan ƙungiyar Ecowas.

“Kafin zuwan Turawa, ƙasashen Afrika ta Yamma ko Ecowas sun kasance ƙasa ɗaya. Ana yin Hausa a kowane yanki ka je kama daga Nijar, Mali, Ghana da sauransu haka ma ga duka sauran yaruka”.

Barau ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da BBC, inda ya ce ya zama wajibi Ecowas ta haɗa kai domin samun ci gaba da ya kamata.

Hajjin Bana: NAHCON ta bayyana adadin maniyyatan Najeriya da za su sauke farali a 2024

“Bayan zuwan Turawa ne suka raba kawunanmu, kuma ya kamata mu haɗa kai yanzu,” in ji Barau.

Ya ce idan ana haɗe za a fi samun ci gaba, walwala da kuma jin daɗi na al’umma.

Mataimakin shugaban majalisar ta dattawan, Wanda shi ne Kakakin riko na majalisar ta ECOWAS, ya ce za su yi duk abin da za su iya wajen hada kan mambobin kungiyar ta Ecowas.

Ganduje ya yi martani kan gwamnatin Kano bisa gurfanar da shi a gaban Kotu

Ya kuma ce suna da kudurin ganin an samar da kudi bai-daya na kasashen.

Barau ya ce suna da kudurin kawo tsarin da zai kawo hadin kai ta hanyar tattalin arziki, tsaro da kuma ci gaban yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sabon Rikici Ya Kunno Kai Cikin Jam’iyyar APC a Kano

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Karamin Ministan gidajen da raya burane...

Yadda Manoma a Nigeria ke cigaba da kokawa saboda karyewar farashin kayan abinchi

  Farashin kayan abinci kamar masara, gero da shinkafa na...

Inganta ilimi: Jaridar New Telegraph ta Karrama Gwamnan Kano

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Sanarwa ta musamman ga masu neman shiga aikin dansanda

Hukumar kula da aikin 'yan sanda na Kasa (POLICE SERVICE...