Kantoman Karamar Hukumar Dawakin Tofa ya Kaddamar da Tallafin Abinci ga Mutane 1,610

Date:

Daga Musa Mudi Dawakin Tofa

 

Kantoman karamar hukumar Dawakin Tofa Dakta Kabiru Ibrahim Danguguwa, ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata da masu karamin karfi 1,610 a karamar hukumar don rage musu radadin matsin rayuwa, a ranar Asabar .

Dakta Danguguwa, ya ce tun bayan shigarsa ofis ya san halin matsi rayuwa da al’ummarsa ke ciki kuma suna da manyan kasuwanni biyu (Dawanau da Kwakawaci), hakan tasa ya kirkiri wani tsari da masu gudanar da kasuwanci a gari ya kamata su ji kan al’umma su tallafa musu (Corporate Social Responsibility) .

 

“Mun kafa kwamati mai mutane 11 muka basu sati daya don su lalubo masu gudanar da kasuwanci a karamar hukumar Dawakin Tofa su bada tallafi don a tallafawa mabukata, a jika hantarsu, a cikin watan azumi”. A cewar kantoman

Tinubu ya sauke Sha’aban Sharada daga mukamin da Buhari ya bashi, tare da maye gurbinsa da dan Kano

Tuni kwamatin sun bada rahoton aikinsu, Ya Kara da cewa a karkashin shirin an samar da buhu mai cin kilo 10 na Gero 600, Masara 660, Wake 150, Garin Burabusko dana Tuwo 40 sai Taliya Katan 110 wanda mabukata 1,610 ne za su amfana da tallafin daga mazabu 11 dake karamar hukumar Dawakin Tofa.

 

Bayan ya kaddamar da tallafin ga wasu daga cikin wadanda za su amfana, ya yi kira ga ‘yan kwamatin da za su cigaba da raba tallafin cewa su tabbatar sun rabawa matane masu matukar bukata, a ko’ina suke, a fadin karamar hukumar Dawakin Tofa, ba tare da nuna bambacin siyasa ko addini ba, soboda ita harkar ciyarwa bata da addini, bata da siyasa inji Dakta Danguguwa.

Har yanzu Nijar taki Bude Bodarta da Nigeria

Shugaban kwamatin kuma shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa Honarabul Surajo Ahmad Chedi ya ce mutane da dama ne suka bada tallafin daga cikinsu akwai rukunin ‘yan asalin karamar hukumar Dawakin kuma ‘yan kasuwa da suka hadar da: Anas Muktar Bello Danmaliki Taliya Katan 100, Alhaji Hudu Joben Marke #1,000,000, Alhaji Sule Ukulliya #500,000 da sauransu. Kana daga cikin rukunin ‘yan Kasuwar Dawanau akwai: Mustapha Mai Kalwa Masara Buhu 20, Alhaji Sani Giredi #1,000,000, Alhaji Yusuf Danhajiya #1,000,000, Saminu Sharifai #100,000 sai Kungiyar ‘Yan Ridi #500,000 da sauransu.

Honarabul Surajo Chedi ya kuma umarci wakilan kwamatocin da za su cigaba da rabon tallafin a dukkannin mazabu 11, cewa su mika sunayen wadanda za su ci gajiyar shirin tallafin abinci ga Jabiru Ahmad Sarauniya domin basu shaidar sahalewa karbar tallafin, kana ya godewa duk wadanda suka tallafa da kudi ko abinci a matsayin sadaka don ganin an dabbaka shirin da sabon kantoma Dakta Kabiru Ibrahim Danguguwa ya bujuro da shi.

Hon. Surajo Chedi ya karkare da cewa gwamnatin karamar hukuma da ta jiha da ta taraiya da kila Danmajalisar taraiya suma za su bada nasu tallafin abinci.

Taron kaddamar da tallafin abincin ya gudana cikin babban dakin taro na cibiyar gudanar da harkokin addinin Musulunci dake karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...