Cushe: Hatsaniya ta kaure a Majalisar Dattawan Nigeria

Date:

 

Hayaniya ta kaure a zauren Majalisar Dattawan Nigeria yayin da sanatoci ke muhawara kan zargin cushe a cikin kasafin kuɗin ƙasar, wanda shugaban ƙungiyar sanatocin arewa, Abdul Ningi ya yi a wata tattaunawa da sashen Hausa na BBC.

Tun da farko shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar Sen. Olamilekan Adeola daga jihar Ogun ya gabatar da ƙorafi kan tattaunawar da Sanata Ningi ya yi da sashen Hausa na BBC.

Ya soki lamirin kalaman Sanata Ningi kan cewa ana amfani da kasafin kuɗi iri biyu a ƙasar.

Sanata Adeola ya ce wannan tamkar cin zarafi ne da kuma ƙazafi.

Ya bayyana cewa kalaman sanata Ningi ba gaskiya ba ne, kasancewar tun asali babu kuɗin da aka ware a wasu ma’aikatu a cikin kasafin kuɗin da majalisar ta amince da shi.

Sai dai Sanata Adamu Aliero daga jihar Kebbi ya bukaci shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio ya yi adalci wajen jin tabakin Sanata Ningi kan kalamansa a hirarsa da BBC Hausa.

A lokacin da ya yi sa’ilin muhawarar, Sanata Abdul Ningi ya bayyana cewa an yi wa kalaman nasa mummunar fassara ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnan Kano ya Naɗa Ahmed Musa a Matsayin Janar Manaja na Kano Pillars

Daga Zakaria Adam Jigirya   Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Yanzu:yanzu: Gwamnan kano ya yi sabbin nade-naden mukamai

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Gwamann jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Yara ɗalibai na fuskatar barazanar daina zuwa Makaranta a Hotoro saboda lalacewar hanya

Daga Isa Ahmad Getso   Al'umma da Malaman makaranta a unguwar...

Kotu ba da umarnin mayar da Natasha bakin aikinta

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Majalisar...