Daga Mubaraka Aliyu Abubakar
Kasar Saudiyya ta sanar da ganin jinjirin watan Ramadan na Shekarar 1445 Bayan Hijra a Yau Dinnan.
Kadaura24 ta rawaito, za a fara Azumin bana a kasa mai tsarki daga gobe Litinin.
Yadda Kalaman Abba Hikima akan Gwamnatin Kano suka tada kura a dandalin sada zumunta
Kafar yada labarai ta Haramain Sharifain dake kasar Saudiyya ce ta Sanar da hakan a Sahihin shafinta na Facebook da X wato Twitter.
Dama dai yau lahadi ne 29 ga Watan sha’aban Kuma ita Ranar da Mai alfarma sarkin Musulmi ya bada Umarnin a fara duban jinjirin watan duban wata a Nigeria.