Yadda Kalaman Abba Hikima akan Gwamnatin Kano suka tada kura a dandalin sada zumunta

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Shahararren lauyan nan Barr. Abba Hikima fagge yayi wasu kalamai da safiyar wannan rana ta lahadi , kalaman da suka tada hazo a shafukan sada zumunta musamman Facebook.

Kalaman da lauyan ya rika yi dai suna da alaka da gwamnatin jihar Kano, wanda hakan tasa wadanda suke goyon bayan gwamnatin suke ganin kalaman Abba Hikiman a matsayin cin zarafin a gare su.

Lauyan dai ganin zabe ana ganin yana cikin yan gaba-dai-gaba-dai na tafiyar Kwankwasiyya saboda gudunnawar da ya bayar kafin zaɓen lokacin zaɓen da bayan zaɓen.

Tinubu ya Baiwa Kwastam Sabon Umarni kan yan kasuwar da aka kwacewa kayan abinchi

Ga dai kalaman da Abba Hikima yayi a sahihin shafinsa na Facebook.

“Na Ɗaya (1).

Kamar na sani, ana gobe za’a rushe shagunan Masallacin Idi, na faɗa masa baki da baki cewa, ranka ya dade, wannan rusau ɗin da ake yi a Kano, akwai buƙatar bin doka da kare haƙƙin mutane. Saboda a lokacin muna kotu akan irin wannan case din da tsohuwar gwamnati.

Sai aka ce dani “ku nemo hanyoyin da zaku kare gwamnati kawai”

Daga ranar na yanke shawarar ba zan karɓi muƙamin su ba. Domin sai yadda akayi dani”. Inji Abba Hikima Fagge

Bayan wasu mintuna kuma Abba Hikima ya sake yin wani rubutun kamar haka:

Yadda za ku kula da kanku a lokacin azumin Ramadan

“Na biyu (2).

Kwanaki kaɗan bayan rushe shagunan masallacin Idi, kuma bayan na bada shawara a sirrance ba a bi ba. kwatsam sai ji nayi an rushe shatale-talen gidan gwamna, saboda haka nayi rubutu a fili nace “now this is wrong” wallahi kasa da minti 30 gwamna ya kira ni yace “ya kayi mana haka”?

A sannan na ƙara jaddawa kaina cewa wannan tafiyar indai bata gyaru ba, to ba tawa bace” . A cewar Abba Hikima Fagge

Wadancan kalamai dai sun zanyo cheche-ku-ce a dandalin sada zumunta na Facebook, Inda wasu suke ganin kalaman Abba Hikiman suna bisa turba wasu kuma suke ganin yana yin kalaman ne saboda ya rasa makoma ko mukami a gwamnatin jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnan Kano ya Naɗa Ahmed Musa a Matsayin Janar Manaja na Kano Pillars

Daga Zakaria Adam Jigirya   Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir...

Yanzu:yanzu: Gwamnan kano ya yi sabbin nade-naden mukamai

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Gwamann jihar Kano Alhaji Abba Kabir...

Yara ɗalibai na fuskatar barazanar daina zuwa Makaranta a Hotoro saboda lalacewar hanya

Daga Isa Ahmad Getso   Al'umma da Malaman makaranta a unguwar...

Kotu ba da umarnin mayar da Natasha bakin aikinta

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Majalisar...