Daga Abubakar Sa’eed Sulaiman
Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ba wa masu yawon ta-zubar, da aka fi sani da ’Yan Kwalta wa’adin mako biyu su tuba ko kuma hukumar ta murkushe su.
Sheikh Aminu Daurawa ya ba da wa’adin ne jim kadan bayan ya dawo kan mukaminsa, bayan sun sasanta da gwamnan Abba Kabir yusuf, wanda kalamansa na sukar samamen Hisbah kan ’Yan Kwalta suka sa shugaban hukumar ya yi murabus.
Malam Aminu Daurawa ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da gidan Radio BBC.
Sheikh Aminu Daurawa ya ce na baiwa bata-garin, “Sati biyu kacal ga ‘yan kwalta ko ku tuba ko Hisbah ta murƙushe ku.”
A ranar Litinin da dare ne dai aka sasanta Sheikh Daurawa da Gwamna Abba a wani zama da Majalisar Hadin Kan Malamai da Kungiyoyin Jihar Kano ta jagoranta a gidan gwamnatin jihar.
Yanzu-yanzu: Sheikh Daurawa ya Amince Zai Koma Bakin Aikinsa
Sheikh Daurawa yace sun tanadi wani fom a hukumar ta Hisbah mai suna na tuba, don haka yace duk wani mai yawon bariki indai yasan da gaske yake to yaje hukumar domin cikewa, su kuma zasu koya masa sana’a sannan a bashi jari don ya dogara da kansa.
Yace gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin zai baiwa hukumar goyon bayan tare da samar musu da kayan aiki don inganta aiyukan nasu.
” Dama gwamnatin bata karɓi takarda ta ta barin aiki ba, sannan mai girma gwamnan ya rokeni cewa in cigaba da zuwa ofis domin a kwau da shaidan din da ya kitsa abubunwan da suka faru, kuma insha Allahu ya yi alkawarin zai baiwa hukumar Hisbah cikakken hadin kai dari bisa dari”. A cewar Malam Daurawa
Yace Babu wani takunkumi da aka sanyawa hukumar face ma, karfafa musu gwiwa da aka ce za’a yi dari bisa dari , don haka Ina fada Maka wannan abu ya faru kamar taki aka sanya mana kuma zamu cigaba da gudanar da aikinmu ba sani ba sabo.
Muhimmiyar Sanarwa Daga Rundunar Yan Sandan Jihar Kano
“Don haka duk wadanda suke ganin su yan Daudu ne da karuwai da fasikai duk wanda yake so zai tuba mun bashi sati biyu ya tuba, wanda kuma yake ganin ba zai tuba ba, to gara ya tattara kayan sa ya bar kano domin kano ba matattarar badala bace”. Inji Malam Aminu Daurawa
Dangane da shawarwarin da gwamnan Kano ya baiwa hukumar na gyara yadda take kamenta , wanda shi ya jo Malam Daurawa yayi Murabus, shehin Malamin yace zasu gudanar da an gyare-gyare don su inganta aiyukan su.
” Insha Allah yanzu za mu dauki matakai guda 4 domin a kara inganta aiyukan ma’aikatan , na daya horar da ma’aikatan , na biyu zamu yi kokarin kafa makarantar Mai suna Hisbah Training school wadda za’a rika yin Diploma da NCE har ma Digiri akan aikin Hisbah, sannan na uku shi ne zamu kara inganta aiyukan ta bangaren karatu da kuma kwarewa , za kuma mu samar da shashin Shari’a da sashin fasahar sadarwa duk a hukumar don kara inganta aiyukan mu “.