Barazanar Tsaro: Karamar hukumar Gwarzo ta Nemi Hadin Kan Jami’an Tsaro

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Majalisar karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano ta yi kira ga jami’an tsaro da sauran jama’a da su ba da hadin kai tare da daukar matakan shawo kan matsalar tsaro da ke addabar jihohin da ke makwabtaka da ita.

Daraktan gudanarwa na karamar hukumar Gwarzo Alh. Ubale Magaji ya yi kiran a lokacin da yake jawabi yayin wani taron tsaro da kwamishinan ‘yan sandan jihar da sauran hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a yankin.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran shiyyar Gwarzo1 Rabi’u Ibrahim Khalil ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.

Cikakken Bayanin Yadda Shari’ar Murja Kunya ta Gudana Yau a Kotu

Ya kara da cewa, karamar hukumar Gwarzo tana fuskantar kwararar ‘yan bindiga da ‘yan fashi da makami domin tana kan yankin Zamfara da Katsina, don haka akwai bukatar a kara inganta hadin gwiwa da bada bayanan sirri a tsakanin jami’an tsaro domin dakile duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Alh.Ubale ya bayyana cewa, gwamnatin jihar Kano mai ci a halin yanzu a karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf ya umurci kananan hukumomin da su kara sanya ido kan harkokin tsaro tare da hada kai da masu ruwa da tsaki wajen kai rahoton duk wata barazanar tsaro domin daukar matakin da ya dace.

“Muna aiki a yanzu don tsara yadda ya kamata da kuma ba da karfi ga yan vigilante da kuma ba da duk wani tallafi ga jami’an tsaro da ke aiki a yankinmu don inganta ayyukan su,” in ji DPM.

Rundunar Sojin sama ta kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Kano

Da yake jawabi kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano wanda ya samu wakilcin jami’in ‘yan sanda reshen karamar hukumar Gwarzo SP Barau Kassim ya yi kira ga gwamnati da ta samar da motocin sintiri masu inganci ga dukkan jami’an tsaro tare da tallafin isassun kayan aiki.

Haka kuma ya kamata a baiwa kungiyar ’yan banga da mafarauta na gida damar ci gaba da bayar da tallafi ga hukumomin tsaro.

Ya kuma yaba da kokarin Sanata Barau Jibrin na gina sansanin rundunar hadin gwiwa a karamar hukumar Gwarzo.

A nasa bangaren Hakimin Gwarzo Barde Kerarriya Alh. Kabiru Bayero wanda Alh Kabiru Muhammad Gwarzo ya wakilta yayi kira ga jama’a da su tallafawa jami’an tsaro ta hanyar basu bayanan da suka dace da zasu taimaka wajen kamo masu laifi.

A nasa bangaren shugaban sashin aiyuka na musamman Nazir Kabir Matawalle ya bayyana cewa sun sami rahotanni sama da ashirin ne na masu satar shanu da kuma garkuwa da mutane a karamar hukumar Gwarzo.

Nazir Kabir Matawalle ya yaba da irin jarumtakar da jami’an tsaro suka yi wajen dakile da dama daga cikin wannan lamari tare da kame mafi akasarin masu aikata laifin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hakikanin halin da gwamnan Katsina yake ciki, bayan wani hatsari

  Rahotanni daga Katsina na cewa gwamnan jihar Katsina Dikko...

Zargin almundahana: ICPC ku fita daga harkokin Siyasar Kano – Kungiyar Ma’aikatan KANSIEC

Daga Hafsat Abdullahi Darmanawa   Kungiyar ma'akatan wucin gadi da suka...

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...