Majalisar dokokin jihar Kano ta bankado badakalar kudi a wasu hukumomin gwamnati

Date:

 

Majalisar dokokin jihar Kano ta bankado badakalar kudi a hukumar Karota da wasu hukumomin gwamnatin jihar.

Majalisar ta bukaci hukumar Karota ta mayar da fiye da naira miliyan 257 zuwa asusun gwamnatin Kano.

Cikin hukumomin da aka nemi su mayar da kudin sun hada da hukumar lafiya a matakin farko da zata mayar da fiye da naira miliyan 2 sai hukumar dab’I da zata mayar da fiye da naira miliyan 1.

Wannan ya biyo bayan rahoton kwamitin kula da kashe kudaden gwamnati da kwamitin ya gabatar na shekarar 2021 a zaman majalisar ranar Litinin

Cikakken Bayanin Yadda Shari’ar Murja Kunya ta Gudana Yau a Kotu

Cikin shawarwarin da kwamitin ya gabatar karkashin shugaban sa Tukur Muhammad Fagge, ya bukaci hukumomin da su mayar da wadannan kudade da suka yi batan dabo.

Haka zalika majalisar zata dauki hukunci kan wadanda ake zargi da rashin tafiyar da kudin yadda ya kamata.

Rundunar Sojin sama ta kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Kano

Da yake jawabi ga manema labarai shugaban kwamitin kula da yadda ake kashe kudaden gwamnati dan majalisa mai wakiltar Fagge, Tukur Muhammad, ya ce wannan na cikin rahoton da mai binciken kudi na jiha ya gabatarwa majalisa.

Nasara Radio ta rawaito cewa, Dan majalisar yace duk lokacin da mai binciken kudi ya gama aikin sa yana mikawa majalisa, kuma majalisa tana gayyatar duk ma’aikatar da aka samu da zargin rashin tafiyar da kudi yadda ya dace.

Ya ce idan kwamiti ya kira hukuma ko ma’aikata ta kare kanta ta gaza yin haka to ba abinda ya ragewa kwamiti saidai ya bada shawarar dawo da wadannan kudi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...