Cikakken Bayanin Yadda Shari’ar Murja Kunya ta Gudana Yau a Kotu

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Kotun Shari’ar Musulunci da ke zaman ta unguwar gama PRP, karkashin jagorancin Khadi Nura Yusuf Ahmed, ta bayar da umarnin a kai shahararriyar yar Tiktoker din nan mai suna Murja Kunya asibitin Gwamnati domin auna lafiyar kwakwalwa ta.

Wadda ake tuhumar mazauninyar unguwar Tishama Hotoro ce a Kano, yana fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume uku da suka hada da tada hankalin jama’a, kalaman bidala da kuma razana al’ummar unguwar da take.

Da yake yanke hukunci, Alkalin Kotun, Malam Nura Yusuf-Ahmad, ya bayar da umarnin a kai wacce ake kara zuwa asibitin gwamnati domin a tabbatar da lafiyar kwakwalwarta saboda zargin da ake yi mata na shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Kotu ta Yanke Wa Ramla Yar TikTok Hukunci Bisa Laifuka Uku

“A zaman kotun daya gabata alamu sun nuna cewa ba ta cikin hayyacinta saboda zargin ko ta sha miyagun kwayoyi.

“Hukumar Hisbah ta rika sanar da kotu lokaci zuwa lokaci akan lafiyarta har tsawon wata uku”.

Yusuf-Ahmad ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa 20 ga watan Mayu 2024 .

Tun da farko, Lauyan mai gabatar da kara, Barista Aliyu Abideen, ya ce hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wadda ake kara bayan ta samu korafe-korafe da dama daga jama’a.

Ya yi zargin cewa Murja Kunya da ake tuhumar ana zarginta da kai bata gari maza zuwa unguwar Tishama tare da Shan miyagun kwayoyi da tsakar dare, sannan kuma suna damun al’umma ta hanyar tayar da hankali da amfani da kafafen sada zumunta wajen dagula al’umma.

“Wanda ake tuhuma a daya daga cikin faifan bidiyonta na Tiktok wanda ya yadu ta bayyana cewa ita ce shugabar duk karuwai a cikin garin Kano.”

Akwai lauje sakin tuhumamme tsakanin Gwamnati, Banggaren Sharia da Hisbah

Sai dai Murja Kunya ta musanta ruhume-tuhume da ake yi mata.

A cewar mai gabatar da kara, laifukan da ake Zargin ta sun ci karo da sashe na 341, 275 da 227 na dokar shari’ar Musulunci ta jihar Kano.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa Hukumar Hizba ta jihar Kano ce ta kama Murja Kunya tare da miƙa ta ga jami’an tsaro bisa zargin ta da laifukan da suka shafi baɗala a shafukan sada zumunta.

Kwamandan hukumar ta Hizba a jihar, Sheikh Ibrahim Daurawa ya ce tuhume-tuhumen da ake yi wa Murja Kunya sun haɗa da: Razana al’umma, ayyukan baɗala, tayar da hatsaniya, tayar da hankalin al’umma, kawo ɓata-gari cikin unguwa da kuma iƙirarin cewa ita ce shugaban karuwai da ƴan kwalta.

Batun kamawa da tura fitacciyar ƴar tiktok ɗin zuwa gidan yari ya ja hankalin al’ummar a jihar ta Kano.

Haka nan labarin fitar da ita daga inda kotu ta tura ta, wato gidan gyaran hali shi ma ya janyo muhawara mai zafi a jihar.

A ranar Litinin gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ba ta da hannu a sakin ƴar tiktok ɗin daga gidan yari bayan umarnin da kotu ta bayar na tsare ta.

Sai dai abun mamaki duk da an rasa inda Murja Ibrahim kunya take , bayan fitar da ita daga Gidan Gyaran Hali sai gata ta bayyana a gaban kotun a wannan rana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...