Sarkin Kano ya Zama Uban Jami’ar Al-Istiqama ta Sumaila

Date:

Daga Khadija Abdullahi Umar

An nada Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a matsayin uban jami’ar Al-Istiqama dake garin Sumaila a jihar Kano.

Shugaban Jami’ar Hon. Abdulrahman Kawu Sumaila ne ya gabatar da takardar nadin ga Mai Martaba Sarkin Kano a ranar Larabar nan.

Da yake mika takardar ga Mai Martaba sarkin Kawu Sumaila yace sun yi la’akari da kwarewa kogewa da Sarkin yake dasu tare da kokarin da yake yi wajen inganta harkokin Ilimi a jihar Kano da Kasa baki daya.

A Jawabinsa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya nuna farin Cikinsa tare da bada tabbacin Zai yi duk mai yiwuwa wajen cigaban Jami’ar dama Ilimi baki daya.

Mai martaba sarkin ya bukaci mawadata dake cikin al’umma da su mai da hankali wajen bada tasu Gudunmawar don cigaba Ilimi a Kano da Kasa baki daya

23 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: An zabi sabon shugaban jami’ar Bayero BUK

Daga Rahama Umar kwaru   Farfesa Haruna Musa ya zama sabon...

An sake sauya lokacin jana’izzar Aminu Ɗantata – Gwamnatin Nigeria

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta ce Hukumomi a Kasar Saudiyyar...

Fadan daba: ku fito ku Kare Kan ku da iyayenku – Gwamnatin Kano ga matasa

Ku tashi ku Kare kanku da iyayen Gwamnatin jihar kano...