Jaridar kadaura24 ta gudanar da rahotanni masu tarihin yawa a shekara ta 2023 da take dab da karewa a wannan rana ta lahadi.
Kadaura24 ta bibi rahotanni 3 mafi tafiri ga al’umma da gwamnati ,Inda suka bada gudunnawa wajen tallafawa al’umma da kuma yin abubuwan da suka dace musamman daga bangaren gwamnati.
Rahoto na farko:
A ranar 15 ga watan mayu, 2023, jaridar kadaura24 ta yi wani rahotanni na jami’ar Yusuf Maitama Sule dangane da yadda dalibai da dama suka kusa rasa damar karatu a jami’ar sakamakon rashin biyan kudin makarantar.
Bayan rahoton da kadaura24 ta yi, an sami cigaba sosai domin hukumar jami’ar ta kara wa’adin lokacin biyan kudaden, wanda hakan ya bada dama ga da yawa daga cikin daliban jami’ar wajen biyan kudin.
Sannan kuma a Sanadiyar rahotanni an sami wasu bayin Allah da suka taimaka wajen biyan kuɗin makarantar ga da yawa daga ciki daliban jami’ar ta Yusuf Maitama Sule.

Babu shakka ya zama wajibi mu yabawa mutane da suka taimaka daliban jami’ar wajen biyan kudaden, Sannan mu mika sakon godiya ga hukumar gudanarwar jami’ar Yusuf Maitama Sule bisa kara wa’adin lokacin biyan kudaden da kuma yadda biya wa wasu dalibai kuɗin makarantar.
Rahoto na biyu :
A ranar 16 ga watan afirilu na shekara ta 2023 jaridar kadaura24 ta buga labari akan wani koke da mutanen da suke gudanar da Sana’a a tashar malam kato sukai na yunkurin sayar da tashar.
Bayan bibiyar labarin da kadaura24 ta yi , ta gano cewa ba gwamnatin jihar kano ce take so sayar da tashar ba, hakan kuma yasa Gwamnatin ta Ankara cewa wasu yan damfara na nema sayar da tashar ta malam kato.
Da dumi-dumi: Tinubu Za yi Jawabi ga Yan Nigeria
A dalilin rahotanni gwamnatin jihar kano ta dauki matakan da suka dace domin hana yan damfarar sayar da tashar, wanda hakan yasa al’ummar da suke neman abinchi a tashar suka sami kwanciyar hankali da lumana.
Rahoto uku :
A ranar 20 ga watan Disamba 2023 , jaridar kadaura24 ta gudanar da wani labarin wanda ake zargin tsohon shugaban gidan Radio kano da sayar da wasu kayiyaki mallakin gidan Radio.
Babu shakka rahoton yayi tasiri wanda hakan yasa gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya dakatar da tsohon shugaban gidan Radio, tare da nada wanda yake kai a halin yanzu.
Sai dai mun fuskanci kalubale sosai kan wannan rahoton, amma dai daga karshen tunda mun san ba kage mukai ba Muna ganin hakan a matsayin wata nasara ta saitawa shugabanni zama da kuma zaburar da su wajen rike gaskiya.
Babu shakka akwai rahotanni da yawa da muka yi wadanda suka taimakawa al’umma daban-daban, daga cikin su ne muka tsakuro wadannan guda ukun.