Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar PDP, Alhaji Sadik Aminu Wali ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar PDP na kasa da su dauki mataki akan tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike saboda abubun da yake yi na haifar da rudani a jam’iyyar.
Sadiq Wali ya yi wannan kiran ne a ranar Asabar a wani taron manema labarai a Kano.
A cewarsa, matakin na Wike ya riga ya yi wa jam’iyyar illa ta hanyar yin adawa da ita, wanda ya kai ga rasa zaben shugaban kasa na 2023.

Ya ce dole ne shugabannin jam’iyyar su yi aikinsu ta hanyar yin abin da ya dace wajen takawa Wike birki, tun kafin lokaci ya kure saboda ba shi da wata kima a jam’iyyar.
“Ya kamata shugabannin PDP su takawa Wike birki ta hanyar dakatar da shi ko kuma korar shi daga jam’iyyar. Mafi munin abun da zai tuni ya riga ya yi. Mun sha kaye a zaben shugaban kasa na 2023 saboda abubunwan da suka yi. Gwamnonin G5 sun hada kai suka yanke shawarar yakar jam’iyyarmu. Menene amfaninsu? A kasar Hausa ana cewa gara a baiwa mutum naira daya idan ya bukata da a ba shi naira goma lokacin da ba ya bukata, domin a lokacin da ya ke bukata, naira daya ta fi masa daraja. ”
Da dumi-dumi: Gwamnan Kano Abba Kabir ya Fashe da Kuka Yayin Wani Taro a Gidan Gwamnati
Don haka muna bukatar mu magance wannan rikicin. Shugabancin jam’iyyar mu, ba duka nake la’antarsu ba, amma kamata su tashi tsaye wajen sauke nauyin da ke kansu. Wannan ba wasa ba ne. Dole ne shugabannin jam’iyyar mu su dauki mataki tun kafin lokaci ya kure. Idan ana maganar kafa kwamitin sulhu, sulhu ake me? Dukanmu mun san abin da ya faru. Gwamnonin G5 karkashin ministan Wike sun yaki jam’iyyarmu. Ba ku buƙatar ku je ku kafa kwamiti don gano abin da ya faru.”
Yakamata Kungiyar Gwamnonin PDP su goyi bayan Gwamna Fubara don samun damar tsayawa da kafafunsa . Na yi imani wike ya bada gudunnawa wajen zaman Fubara gwamna, amma yanzu dai shi Allah ya baiwa mulkin jihar Rivers, don haka ya Kamata a bar shi yayi abun da ya dace. t
A lokacin da yake mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan tsohon kakakin majalisar wakilai, Alhaji Ghali Umar Na’abba, Sadik Wali ya bayyana Na’abba a matsayin shugaba jajirtacce kuma mara tsoro wanda ya tsaya kan gaskiya.
“Gali Umar Na’abba yana daya daga cikin fitattun ‘yan siyasa da ke fadin gaskiya ga hukumomi ba tare da tsoro ko son rai ba. Idan kun yi kuskure a harkokin mulki ko siyasa, yakan kira ku ya gaya muku gaskiya ba tare da la’akari da kabilanci ko addini ba.”