Ganduje ya wakilci Tinubu a wajen taron rufe musabakar Alkur’ani ta kasa a Yobe

Date:

Daga Hafsat Lawan Sheka

 

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya wakilci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen rufe musabakar kur’ani mai girma ta kasa ta 2023.

Gidauniyar dake kula da Musabaqar karatun kur’ani a Najeriya, cibiyar nazarin addinin musulunci ta Jami’ar Usman Danfordiyo dake Sokoto da kuma gwamnatin jihar Yobe ce suka dauki nauyin shirya taron wanda aka gudanar a Yobe.

Talla

Zainab Aliyu Muhammad daga jihar Kano ce ta zama zakara a bangaren mata a musabakar, yayin da dan jihar Bauchi Ibrahim Muhammad Nasir ya zama zakara a bangaren maza na musabakar .

Sai dai gidauniyar Ganduje ta bayar da tallafin Naira miliyan 10 ga wadanda suka yi nasara da kuma wadanda suka shirya gasar.

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano Abba Kabir ya Fashe da Kuka Yayin Wani Taro a Gidan Gwamnati

Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban mai taimakawa shugaban Jam’iyyar APC na kasa kan harkokin hotunan masu motsi da taruka Aminu Dahiru, ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.

Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe, Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar II, Sarakunan gargajiya, manyan ‘yan siyasa, da sauran manyan baki ne suka halarci taron.

Dr Abdullahi Umar Ganduje ya samu rakiyar tsohon mataimakin sa, Dr Nasiru Yusuf Gawuna, mataimaki na musamman ga shugaban kasa Tinubu kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari, Hon. Aminu Sani Jaji memba mai wakiltar mazabar Kauran Namoda/Birnin Magaji ta jihar Zamfara da Alhaji Lawan Garba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...