Tunzura jama’a: Gamayyar wasu Kungiyoyi sun yi kira da a kama Ganduje

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

Gamayyar wasu kungiyoyin masu ruwa da tsaki a jihar Kano a kan rashin adalci sun bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta cafke shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje bisa zargin tunzura jama’a.

An yi wannan kiran ne a yayin wata zanga-zangar lumana da addu’a ta musamman da masu ruwa da tsaki a kan rashin adalci suka shirya, karkashin jagorancin Dakta Idris Salisu Rogo, a karamar hukumar Rogo ta jihar Kano.

Gamayyar kungiyoyin ta nuna damuwarta kan shari’a da ake ta tafkawa ta zaben gwamnan jihar Kano, lamarin da ke sanya shakku kan rashin adalci sanya bangaren shari’a a tsaka mai yuwa.

Talla

Sun yi karin haske kan al’amuran da jiga-jigan jam’iyyar APC da suka hada da shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, suka yi game da sakamakon hukunce-hukuncen kotuna wanda daga baya abun da suka fada yake tabbata a hukuncin kotun.

Kungiyar ta kuma nuna fargaba kan wasu shirye-shirye da jam’iyyar APC ke yi wanda zai iya yin tasiri a shari’ar zaben gwamnan Kano ta bangaren shari’a, wanda ake zargin cewa za a yi haka ne Shugaba Tinubu damar sake tsayawa takara a 2027.

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano Abba Kabir ya Fashe da Kuka Yayin Wani Taro a Gidan Gwamnati

Sun kuma jaddada bukatar kotun kolin Najeriya ta tabbatar da adalci ta hanyar tabbatar da cewa wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano a 2023, Abba Kabir Yusuf, a bar masa mukaminsa.

Bugu da kari, sun bukaci bangaren shari’a da su kare martabar da suke da ita ta hanyar hana wadanda ke da alaka da cin hanci da rashawa ta’ammali da mutuncin su.

Kungiyar ta jaddada cewa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai iya samun goyon bayan al’ummar Kano ne kawai ta hanyar bari ayi adalci da kuma ci gaba da nuna rashin son kai a hukuncin da kotun koli zata yanke kan zaɓen gwamnan Kano.

Sun bayyana gamsuwarsu da yadda shugaba Bola Tinubu yake da niyyar tabbatar da dimokuradiyya tare da bukatar shi da ya bari a yi adalci.

Bugu da kari, sun yi gargadin cewa duk wani yunkuri na kwaceww Abba Kabir Yusuf mulkin sa zai iya kawo cikas ga tsaron kasa, lamarin da ya kamata ‘yan Najeriya masu kishin kasa su yi kokarin gujewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...

Rikicin Masarautar Kano: Kotu ta Sake Sabon Hukunci

A wani sabon yanayi na rikicin Masarautar Kano, Kotun...

Gidauniyar Aliko Dangote za ta rabawa ‘yan Najeriya miliyan daya shinkafa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gidauniyar Aliko Dangote ta raba buhunan...

Rufe Makarantu da azumi: Ministan Ilimi ba ta da ilimin harkokin mulki – Jafar Sani Bello

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano...